1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana sukar gwamnan Zamfara kan rufe kafofin labarai

October 17, 2022

Hukumomi da ke kula da kafafen watsa labarai dama sauran al'ummar Najeriya na ci gaba da sukar matakin gwamnatin jihar Zamfara na rufe kafafen watsa labarai.

https://p.dw.com/p/4IHbs
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle Hoto: Zaharaddeen Umar/DW

Hukumomi da ke kula da kafafen watsa labarai a Najeriya dama sauran al'umma na ci gaba da sukar matakin gwamnatin jihar Zamfara na rufe kafafen watsa labarai mallakin gwamnatin kasar da masu zaman kansu, matakin ya biyo bayan zargin saba dokar aiki a jihar da ke fama da matsalar tsaro mafi muni a yankin arewacin Najeriya.

Kungiyoyi dabam-daban sun bi sahun hukumomin na ganin rashin dacewa kan rufe kafafen watsa labarai musamman a daidai wannan lokaci da ake mulkin dimokaradiyya kamar yadda shugaban hukumar da ke kula da kafafen watsa labaran Najeriya wato NBC Balarabe Shehu Ilela ke cewa, hukumar su kadai keda damar daukar wannan mataki. A cewar Sama'ila Balarabe Malami na Sashen koyar da aikin Jarida na Kwallejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman da ke Katsina ko a yanayi na yaki ba'a rufe kafafen watsa labarai saboda mahimmancin kafar ga al'umma.

Gwamnatin jihar ta Zamfara ta bada umarnin rufe kafafen watsa labaran saboda sun yada gangamin taron dan takarar Gwamnan jihar na Jam'iyyar PDP wanda suka ce, ya sabawa doka saboda sun hana duk wasu taruka na siyasa saboda hare-hare 'yan bindiga da suka haifar da matsalar tsaro da suke fuskanta, amma sai ga shi jam'iyyar ta bijire wa doka ta kuma yi taron wanda har aka hallaka mutane da dama.

Duk da wadannan ce-ce-kuce da suka biyo bayan matakin gwamnatin jihar Zamfarar, kawo yanzu gwamnatin jihar ta Zamfara ba ta ce komai ba kan dage dokar don samun damar sake bude kafafen watsa labaran kamar yadda hukumomin tarayyar Najeriya suka bukaci ta yi.