1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikicin NBC da 'yan jarida

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 2, 2022

Matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka ta hanyar amfani da Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai, na ta dakatar da shirin tattaunawa da gidan radiyon Vision FM ke gabatarwa mai suna "Idon Mikiya" ya janyo martani.

https://p.dw.com/p/46QRd
Mosambik - Nampula Rádio Vida
Kafafen yada labarai a Afirka, na fuskantar kokarin dakilewa daga mahukuntaHoto: DW/J. Beck

Gwamnatin Najeriyar dai ta hannun Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai ta NBC, ta dakatar da shirin tattaunawar na gidan radiyon Vision FM mai suna Idon Mikiya har na tsawon watanni shida. Baya ga haka kuma, gwamnatin ta ci tarar gidan radiyon zunzurutun kudi Naira miliyan biyar bisa zargin saba kaida. Hukumar ta NBC ta Najeriya dai, ta bayyana matakin a matsayin ladabtarwa kan laifin da ta ce gidan rediyon ya tafka a shirinsa na "Idaon Mikiyar" da ya tattauna batutuwa da suka shafi tsaro da cin hanci da rashawa da aka yi a Hukumar Leken Asiri ta kasar wato NIA. Shirin dai ya tabo batun wasu makudan kudi da aka gano a wani gida a Ikoyi, inda lamarin ya zama na a ci shiru da kuma batun nadin shugaban hukumar.

Najeriya I Ziyarar Peter Limbourg a Lagos
Gidan talabijin na Channels, na zaman guda daga cikin abokan huldar DW a Najeri Hoto: DW/K. Bergmann

Tuni dai 'yan Najeriya suka fara mayar da martani musamman wadanda ke amfana da shirin na "Idon Mikiya," a sassan kasar ciki har da Abuja. Ana dai samun karuwar daukar irin wannan mataki a kan kafofin yada labarai a Najeriyar, kama daga matakin da aka dauka a kan tashoshin AIT da kamfanin jarida na Daily Trust zuwa ga gidan talabijin na Channels da kuma yanzu an kai ga radiyon Vision FM ya janyo saka ayar tambaya. Shin ko mataki ne na gyara aikin jaridar ko kuwa toshe bakin 'yan jaridu duk da sanin 'yancin fadin alabarkacin baki da shi ne ginshikin aikin? Da alamun za a ci gaba da ja-in-ja a tsakanin gwamnati da kafofin yada labaran Najeriyar, kan matakin mahukuntan na dagewarsu kan cewa suna gyara ne su kuma suna ganin kokari ne na tsohe 'yancin fadar albarkacin baki da kowane dan kasa ke da shi.