1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe masallata

Binta Aliyu Zurmi
September 24, 2022

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya na cewar wasu ayarin 'yan bindiga sun kai hari a kan masallata a wani masallaci a kauyen Ruwan Jema da ke garin Bukukuyum a jihar.

https://p.dw.com/p/4HIvT
Nigeria | Bello Matawalle
Hoto: Zaharaddeen Umar/DW

Ayarin maharan sun isa harabar masallacin da misalin karfe biyu na rana a gogon Najeriya a kan babura, suka bude wa masallatan  wuta da harbin irin na kan mai uwa da wabi.

Harin da aka kai shi a lokacin sallar Juma'a a jiya nan take mutane 15 suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata.

A watan Augustan da ya gabata sama da naira miliyan 9 mazauna wannan gari na Ruwan Jema suka baiwa 'yan bindigan da alkawarin ba za su kai musu hari ba.

Wannan dai na zuwa ne yayin da a baya-bayan nan dakarun sojin kasar ke fatatakar 'yan bindiga daga dazuzukan da ke jihar ta Zamfara, inda aka gargade mazauna yankunan da su yi kaura zuwa wani wuri.