1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zamfara ta karbi tuban Bello Turji

Binta Aliyu Zurmi
August 23, 2022

Shahararren dan bindigar daji da ya addabi al'ummar jihar Zamfara a Najeriya Bello Turji ya rungumi sulhu da kuma tabbatar da ajiye makamansa. Tuni mahukunta a jihar suka ce sun karbi tubansa

https://p.dw.com/p/4Ftw4
Nigeria | Bello Matawalle
Hoto: Zaharaddeen Umar/DW

Wannan bayani na kunshe ne a jawabin da mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya yi inda ya tabbatar da cewa gwamnati ta karbi tuban dan bindigar.

Mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara Hassan Nasiha ya ce tun bayan da suka cimma matsaya game da tuban dan bindigar, yanzu fiye da makwanni shida ke nan ba a sami asarar rai ba da  ya danganci ayyukan 'yan ta'adda a jihar. 

A watan Yunin da ya gabata ne gwamnan jihar ta Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya umurci mataimakinsa da ya jagoranci tattaunawar sulhu da 'yan bindigar, yanzu haka Turji na sanar da bukatar a sako masa 'yan bindigar da ke hannun gwamnati da kuma kawo karshen kisan da ya ce ana yi wa fulani 'yan uwansa.