1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani bayan umarnin sakin Nnamdi Kanu

Uwais Abubakar Idris RGB
October 14, 2022

Takaddama ta barke a Najeriya kan hukuncin da babbar kotun kasar ta yanke na bayar da umurnin sakin shugaban kungiyar masu ikirarin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.

https://p.dw.com/p/4ICuG
Jagoran kafa kasar Biafra | Nnamdi Kanu
Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi KanuHoto: DW/K. Gänsler

A Najeriya takaddama ta barke a kan hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke inda ta bayar da umurnin a saki shugaban haramtaciyyar kungiyar masu ikirarin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, ita kuma gwamnatin Najeriya ta ce kotu ta sallami Kanu ne amma ba ta wanke shi ba. Karin Bayani: 

NIGERIA Biafra Aba Demonstration
Magoya bayan Nnamdi KanuHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Wannan hukunci da babbar kotu da ke Abuja ta yanke a kan tuhumar da akewa shugaban na haramtacciyar kungiyar masu ikirarin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu dai yana tayar da kura sosai, domin kuwa jim kadan bayan murna da shewa har ma da fara bukukuwa da ‘ya'yan kungiyar suka shiga a kan hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke na sallamar jagoran Kungiyar IPOB. Amma menene zahirin abin da doka ta ce ne a kan wannan hukunci da mai shari’a Jummai Hannatu ta jagoranta da ya zama mai harshen damo? 

Bonn Nigerianer in Bonn protestieren auf dem UN-Campus
Magoya bayan Nnamdi Kanu a BonnHoto: Tobore Ovuorie/DW

Jim kadan dai bayan wannan hukunci ne ministan shari’a kuma Atoni janar na Najeriyar ya fitara da sanarwar da mai taimakawa ministan a kan hulda da jama’a da yada labaru Dakta Umar Gwamdu ya sanyawa hannu, ta ce, kotun ta yanke hukuncin kan batun cafko Nnamdi Kanu ne daga kasar Kenya da Najeriya ta yi, don haka kotu ta sallame shi ne amma ba ta wanke shi daga sauran laifuffuka na zargin aikata ta’adanci da gudu daga belin da aka ba shi.

Tuni dai kungiyoyi masu zaman kansu irin ta gamayyara kungiyoyin fararen hula na arewacin Najeriya suka maida martani tare da nuna jayayya. A yayin da ake wannan hali alamu na nuna gwamnatin Najeriyar za ta ci gaba da tuhumar Nnamdi Kanu ko kuma ta daukaka kara a kan batun, domin har yanzu yana garkame a hannun hukumar tsaro ta farin kaya a Abuja. Lauyoyin Nnamdi Kanu na ci gaba da kumfara baki a kan wannan batu da yake daukan hankali a Najeriyar da ma kasashen ketare.