Najeriya: Ci gaba da tsare Nnamdi Kanu
July 26, 2021Duk da marka-marka ta ruwa dai, kotun ta yi cikar kwari da magoya baya da masu kallon shari'ar Nnamdi Kanu da ma masu sana'a ta jarida, domin kallon yadda take shirin kaya wa a shari'ar da ke daukar hankali a ciki da ma wajen kasar a halin yanzu. To sai dai kuma alkalin kotun mai shari'a Binta Nyako ta dage sauraron karar, har ya zuwa ranar 21 ga watan Oktobar wannan shekara, domin tafiya hutun alkalan daukacin kasar. Koda ya ke Kanun da ke tsare a hannun hukumar farin kayan cikin gida DSS bai bayyana a gaban kotun ba, sakamakon abun da hukumar ta kira rashin cikkaken shiri.
Karin Bayani: Kama masu rajin kafa kasar Biafra
A cikin watan Yuninda ya gabata ne dai, jami'an tsaron Tarayyar Najeriyar suka kamo madugun daga Kenya, suka kuma gurfanar da shi gaban kuliya domin ci gaba da shari'ar da ya tsallake ya tserewa a baya. Sai dai daga dukkan alamu kasa gabatar da shi gaban kuliyan ya kona ran da dama, kama daga lauyoyinsa ya zuwa ragowar 'yan kungiyar IPOB din da suka mamaye harabar kotun domin sauraron yadda take shirin kayawa. In har lauyoyin Kanu na tunanin da biyu dai, da kyar da gumin goshi jami'an tsaron da suka mamaye harabar kotun suka iya shawo kan kokari na magoya bayan nasa na isa zuwa zauren shari'ar.
Sai ma da ta kai ga 'yan sanda kamen wasu 'ya'yan kungiyar ko bayan jibge motocin ko ta kwana, kafin samun nasarar tabbatar da zaman kotun da ke zama na biyu tun bayan sake kamo jagoran masu rajin ballewa da kafa kasar Biafra daga Tarayyar Najeriyar. Mr Okoli dai na zaman dan kungiyar IPOB din da kuma ya ce, yaudara a bangare na hukumomi ne ya sa jami'an tsraon hana su shiga kotun da ma kasa gabatar da Kanun a gaban kuliya. Yaudara da sunan shari'a ko kuma neman murde wuyan 'yan mulki dai, gwagwarmayar Biafran na daukar fasali na tattalin arziki da siyasa.
Karin Bayani: 'Yan sandan Najeriya sun kame 'yan IPOB
Kuma wasu a cikin masu goyon bayan Kanun dai daga dukkan alamu, na fakewa a cikin rikicin makiyaya da manoman da ke rikidewa da sauya launi a sassa dabam-dabam cikin kasar. Ngozi Patrick dai ta iso harabar kotun ne da nufin bacin ranta, dangane da yadda masu kiwon Najeriyar suka hana ta sana'ar gado ta shekara da shekaru. Mahukuntan na Abuja dai na tsakanin biyan bukatar kowa a cikin bakin hadari na siyasa da kuma fuskantar tayar da kayar baya cikin halin babun da ke ta karuwa a Tarayyar Najeriyar a halin yanzu.