1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shirin hana likitoci fita waje aiki

April 7, 2023

Majalisar Wakilai ta amince da dokar da ke shirin tilasta wa likitoci share shekaru biyar a Najeriya kafin samun izinin zuwa kasashen waje aiki.

https://p.dw.com/p/4PpDA
Likitocin Najeriya na ficewa neman aiki a waje
Likitocin Najeriya na ficewa neman aiki a wajeHoto: Nasir Ghafoor/AP/picture alliance

A wani abun da ke iya kai wa ya zuwa sabon rikici a tsakanin gwamnatin tarrayar Najeriya da kungiyar likitocin Najeriyar, Majalisar Wakilai ta kasar ta amince bisa wata dokar da ke shirin tilasta wa likitoci na kasar share shekaru biyar cikin kasar, kafin samun izini na ficewa zuwa kasashe na waje don yin aiki.

Ya zuwa yanzu, akalla likitoci dubu biyu ne ke barin kasar a shekara cikin sunan cin rani. Kuma kwarrarun likitocin tarrayar Najeriya sun yi nisa a kasashen Turai da 'yan uwansu na Gabas ta Tsakiya in da ke zaman sababbin matattarar likitocin da ke fadin ba dadi cikin kasar a halin yanzu.

Najeriya na fama da matsalar karancin likitoci
Najeriya na fama da matsalar karancin likitociHoto: Rodger Bosch/AFP/Getty Images

To sai dai kuma bayan share tsawo na lokaci tana guna-guni a kuryar daki, tarrayar Najeriyar na neman mafita tare da wata dokar da ta tilasta daukacin likitoci na kasar share shekaru guda biyar suna aiki kafin samun izinin damar yin aiki can a kasashe na waje. Dokar da ta tsallaka mataki na biyu na zauren majalisar, na da babban burin kai karshen kaurar likitoci cikin kasar da ke zaman ta kurar baya cikin batun na lafiya.

Duk da dimbin makarantun aikin likita, har ya zuwa yanzu yawan likitoci cikin kasar bai haura dubu 25 ba a tarrayar Najeriyar da ke da mutane miliyan 200 da kadan. Sabuwar dokar ta fara jawo takkadama a tarrayar Najeriyar in da kungiyar likitoci ta kasar NMA ta ce, akai ga kasuwa.

Asibitin Koyarwa na jihar Legas
Asibitin Koyarwa na jihar LegasHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Kungiyar NMA dai ta ce, maimakon a dorawa kare laifin kura, kamata yayi a kalli mai ya janyo maitar tun daga farko. Kyautata tsarin aiki ko kuma kokari na murde wuyar 'yan cin rani dai, kusan kaso sittin cikin dari na likitoci na kasar a fadar kungiayr kananan likitoci na kasar na neman hanyar fita da nufin inganta rayuwa da makomar likitocin Najeriyar.

Ya zuwa yanzun, ikita guda daya ne ke duban marasa lafiya dubu 30 a sashen kudanci na kasa a yayin kuma da adadin ya kai dubu 45 a sashen arewacin kasar.