1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar karancin likitoci a Najeriya

September 7, 2022

A wani abun da ke kara kawo damuwa ga harkar lafiya a Najeriya ana ci gaba da fuskantar kaurar daruruwan kwararrun likitocin kasar zuwa kasashen waje don neman ingantacciyar rayuwa.

https://p.dw.com/p/4GXmX
Asibitin NajeriyaHoto: Reuters

A farkon watanni shida na shekarar bana  kadai dai akalla likitoci 2000  ne suka kauracewa tarrayar Najeriyar zuwa kasashen Birtaniya da Kanada da kuma Saudi Arabiya .

 A wani abun da ke kara tada hankalin kungiyar likitoci ta kasar  da ke dada fuskantar karuwar yawan al'umma da raguwar kwararrun ma'aikatan kula da lafiyar al'umma.

Kama daga kasa biyan albashi a kan kari ya zuwa rashin kayan aiki da ma uwa uba batun rashin tsaro dai kungiyar likitocin kasar dai ta ce aiyukan likitoci na dada fuskantar barazanar da ta tilasta sauyin shekar a cikin neman dai dai.

Matsakaicin albashi na kwararrun  likitoci a cikin kasar dai bai wuci Naira 750,000 ko kuma dala dubu daya a wata, a yayin kuma da suke iya samun dalar Amurka dubu kusan 12 a wata  kasar kamar Bietaniya a cikin wata gudan.

Marasa lafiya a asibiti
Marasa lafiya a asibitiHoto: picture alliance/AP Photo/J. Ola

Abun kuma da ke daukar hankalin likitocin ya zuwa neman sauya rayuwa da kila kokari na kauce wa rikicin babun da ya mamaye harkokin lafiya cikin kasar.

Ya zuwa tsakiyar shekarar bana dai sama da likitoci 9,000 ne daga tarayyar Najeriyar suke aiki a asibitocin kasar Birtaniya, ko bayan wasu dubu hudu da ke kasar Saudiya.

A yayin kuma da yawan likitocin da ke asibitocin kasar suka ragu daga kusan dubu 80 ya zuwa kasa da Dubu 30,000 sakamakon kaurar da ke ta kara karuwa.

Dr Ehinare Osagie dai na zaman ministan lafiya na Najeriyar da kuma ya ce kaurar bata da tasiri ga harkoki na lafiyar al'umma.

"Ita kanta kasar Birtaniya na kukan likitocinta na kaura zuwa kasashen Amurka da na Kanada da Australiya da New Zeland matsala ce da ta shafi ko'ina duniya. A Najeriya a zahiri muna samar da likitoci tsakanin 2000 zuwa 3,000 daga makarantunmu a shekara. Kuma kasa da dubu daya ne ke kaurar, har yanzu muna da likitoci da yawa, matsalar kawai ita ce sun kasa shiga tsarin aikinmu.

A gaskiya ma dai muna da isassun likitoci, sai dai kawai sun kasa shiga tsarin aiki saboda matsalar daukar aiki a jihohi, kuma ita kanta gwamnatin tarrayar ta makale. Rashin ingantaccen tsarin maye gurbinsu ne yasa ake ganin kamar akwai matsalar likitoci a asibitoci na gwamnatin tarraya".

Motar daukar marasa lafiya
Motar daukar marasa lafiyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Duk da rashin ingancin tsarin karatu a jami'o'in tarayyar Najeriyar dai, kasar na nasarar iya horar da kwarrarun likitocin da ke ta kara nuna iyawa a ko'ina a duniya. Kuma ko bayan nan dai Najeriyar na zaman daya a ciki na kasashe na kalilan da ake ilimantar da likitocin kyauta.

Dr Ado Muhammed dai na zaman mashawarcin kasashen D8 na musulmi ga batun na lafiya da kuma ya ce ana bukatar saka kishin kai a cikin tsarin  da ya kai ga samun horon kyauta.

An dai kiyasta kowane likita guda cikin kasar dai a halin yanzu na da jan aikin kulawa da mutane tsakanin 4,000, zuwa 5,000 maimakon 600 da hukumar lafiya ta duniya ta tanada.