1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fiye da likitoci 500 na sha'awar barin Najeriya

Uwais Abubakar Idris AMA
August 26, 2021

A daidai lokacin da likitoci masu neman kwarewa ke cikin yajin aiki sama da 500 na likitocin Najeriya na rige-rigen ficewa daga kasar domin aiki a kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/3zXNA
Nigeria Selbstmordanschlag in Konduga Verlezte im Krankenhaus von Maiduguri
Hoto: Reuters

Kama daga kwararru a fanin koyarawa a jami’o'i har zuwa ga gogaggu a fanin kimiyya da fasaha da ma likitoci ‘yan Najeriya da dama ne ke ci gaba da ficewa daga kasar zuwa kasashen ketare domin aikin da suka kware kuma akai matukar ana da bukatarsu a kasar. Shekaru shida kenan kasar Saudiyya na zuwa Najeriyar domin daukar daukar likitoci, sai dai ba’a taba ganin tururwarsu ba irin a wannan karon inda har da kwararru "consultant" maza da mata duk sun leko kamar haka. 

Karin Bayani: Tirka-tirkar gwamnati da likitoci a Najeriya

Alkaluma daga hukumomin kula da lafiya a Najeriyar sun nuna cewa kasar na da adadin likitoci dubu 35, adadin da ya zuwa yanzu ya ragu sosai saboda yawan ficewa da suke yi zuwa kasashen waje. Alal misali kowane likita daya na kula da ‘yan Najeriya dubu biyar ne maimakon likita daya a kan mutum 600, kamar yadda hukumar lafiya ta bukata. Duk da cewa ra’ayoyi sun sha bamban a kan dalilan barin Najeriyar don zuwa kasar waje aiki ga yawan likitocin, amma duka bori daya suke wa tsafi domin koke ne na tabarbarewar yanayin biyansu kakokinsu.

Nigeria l Nach Protesten in Lagos, Verletzte im Krankenhaus
Hoto: Ademola Olaniran/Lagos State Government/Reuters

Karin Bayani: Makomar fannin kiwon lafiya a Najeriya

Sanin cewa wadannan likitoci na shirin barin Njeriya ne a daidai lokacin da ake fama da yajin aiki, ko wacce illa wannan zai yi ga harakaer kula da lafiya, wasu daga cikin tambayoyin da jama'a ke wa kansu kenan. Ministan lafiya na Najeriyar Chris Ngige ya dage kan cewa Najeriya bata da karancin likitoci, koma dai mene ne ficewar kwararu daga kasar suna gina wata kasa babban kalubale ne ga kasashe masu tasowa irin Najeriya musamman a fanin krwararu masu kula da lafiya.