1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Fulani a kudancin Najeriya

Muhammad Bello LMJ
February 2, 2021

Kungiyar gwamnonin jihohin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, ta sanar da cewar ta kafa dokar hana Fulani makiyaya yin kiwo da kuma hana su keta dazzuzuka ba bisa ka'ida ba a yankin.

https://p.dw.com/p/3omwo
DW Fulani
Fulani kan bi dazuzzuka da gonaki, a kokarinmsu na sama wa dabbobinsu wajen kiwoHoto: DW/K. Gänsler

Jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa ta jahohin Yankin,sai nan da nan kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra wato IPOB, wadda kuma gwamnatin Najeriyar ta haramta ta ce za ta umarci dakarunta na rundunar tsaron da ta kafa a yankin, su fara aikin ganin Fulanin sun bi wannan doka.

Karin Bayani: Cimma yarjejeniyar sulhu da makiyaya

A yammacin ranar Litinin ne dai, kungiyar Gwamnonin Yankin Igbo mai jihohi biyar ta fiatar da sanarwar da ta ce, daga yanzu ba batun Fulani makiyaya su ja zugar shanunsu daga wuri zuwa wuri a yankin musamman ma yadda Fulanin kan fada dazuzzuka da gonaki da nufin yin kiwon dabbobinsu.
Sai dai kungiyar ta Gwamnonin Igbo da gwamnan Ebonyi Mr David Umahi ke jagoranta, ta yi kira da al'ummar yankin baki daya, da su daina saka siyasa a cikin lamarin tsaron Najeriyar baki daya, domin a cewar kungiyar lamarin ba abin wasa ba ne.

Nigeria - Gewalt zwischen Hirten und Bauern
Sauyin yanayi na taimakawa wajen samun rikici tsakanin manoma da makiyayaHoto: Imago/epd/A. Staeritz

Karin Bayani: Samar da matakan magance rikici da makiyaya

Haka kuma kungiyar ta yi kira ga masu yada bayanai da hotuna musamman na bidiyo na karya a kafafen sada zumunta da ke nuna 'yan kungiyar IPOB da ke rajin kafa kasar Biafra, na kashe Fulani makiyaya a yankin Igbo. A baya-bayan nan dai, cece-kuce da rigingimu gami da zargin tashe-tashen hankula da ake danganta su da Fulani makiyayan sun mamaye Najeriya, inda yanzu makiyayan ke neman fada wa yanayi na rashin tabbas.