1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kame wasu 'yan kungiyar IPOB

May 27, 2021

A yayin da ake ci gaba da fuskantar kona ofisoshin 'yan sanda da kisan jami'an tsaro a Kudu maso Gabashin Tarayyar Najeriya, babban sifeton 'yan sanda na kasar ya ce sun kama 'yan kungiyar IPOB da dama dauke da makamai.

https://p.dw.com/p/3u3kn
Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Jagoran masu rajin kafa kasar Biafra daga Najeriya Nnamdi Kanu Hoto: DW/K. Gänsler

Cikin tsawon watanni shidan da suka gabata dai ofisoshin 'yan sanda kusan 25 ne aka kona, baya ga kisan jami'an 'yan sandan 20 a wani abun da ke nuna ta'azzarar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas. 'Yan kungiyar IPOB dai sun yi nisa a wajen neman sake tayar da fatalwar rajin kafa kasar Biafra da ta kwanta dama shekaru 50 da doriya, inda suka kaddamar da sababbin hare-hare a cibiyoyin 'yan sanda da ofisoshi na hukumar zabe da nufin cika burin mallake ikon al'umma a jihohin yankin guda Biyar.

Karin Bayani: Tabarbarewar tsaro a Najeriya

A cikin tsakiyar watan Mayun da muke ciki ne dai, rundunar 'yan sandan Najeriyar ta kaddamar da sabon kamfen na mai da zaman lafiya cikin yankin da ya dauki lokaci yana zaman dan kallo a cikin harkar mulki ta kasar. Akalla karin 'yan sanda 3,700 ne dai, rundunar 'yan sandan Tarayyar Najeriyar ta ce ta tura zuwa yankin na Kudu maso Gabas da nufin tunkarar matsalar da ke zama barazana mai girma har ga makomar zabukan kasar a nan gaba. Kuma a fadar babba na sifeton 'yan sanda na kasar Usman Alkali rundunar na samun ci gaban da ya kai ga kame da dama na 'ya'yan kungiyar, ko baya ga makaman da suka kai kusan 600 a kwanaki 10 da suka gabata. 

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Masu rajin kafa kasar Biafra daga Najeriya, sun jima suna fafutukaHoto: Getty Images/AFP

Ana dai kallon harin da ya mai da kai zuwa 'yan sandan da ofisoshi na hukumar zabe da kokarin hargitsa zabe a cikin yakin da kila ka iya jefa daukacin kasar cikin rudani. To sai dai kuma a fadar babban sifeton, rundunar ta fara bincike bisa dangantakar tashin hankalin da siyasa a kasar. A watan Nuwamban wannan shekara ta 2021 ne dai, aka tsara zaben gwamna a jihar Anambra da ke zaman guda cikin jihohin yankin guda biyar, baya ga kaddamar da kamfen din sake rijistar 'yan zabe a cikin watan gobe na Yuni. Hargitsa lamuran zaben dai, na iya kai kasar ga gaza samun ingantaccen zaben da ya cika sharuddan kundin tsrain mulki na kasar.

Karin Bayani: Fargaba bayan hari a gidan yarin jihar Imo

Ya zuwa yanzu dai rahotannin da ke fito wa daga yankin, na fadin gwiwar 'yan sandan na dada sanyi sakamakon kisan da ke zaman na bazata. A ofisoshi da dama dai, 'yan sandan sun gaza kare kansu balle su kare makamai da kadarorin hukumar daga ayyukan 'yan awaren IPOB din. To sai dai kuma a fadar Usman Alkalin akwai alamun karin gishiri a bisa halin da 'yan sandan ke ciki a yankin na Kudu maso Gabas. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa, a tsakanin matasan IPOB da ke neman ballewar ko ta halin kaka da kuma gwamnatin tarayyar da ke fadin ba a isa ba.