1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikici ya sake barkewa a Filato

January 25, 2024

Kimanin mutane 30 ne suka mutu a jihar Filaton Najeriya a wani rikici da ya sake barkewa a garin Mangu, duk da dokar hana zirga-zirga da gwamnati ta kakaba.

https://p.dw.com/p/4bfeH
Hoto: picture-alliance/dpa

Sabon rikicin na zuwa ne bayan harin da aka kai na ranar Kirismetin bara wanda ya yi sanadin rayukan mutane a kalla 140. Guda daga cikin shugabannin yankin ya ce, maharan sun far wa wasu garuruwa ne da ke iyaka da kananan hukumomin Mangu da kuma Barkin Ladi.

Wadanda suka tsallake rijiya da baya sun bayyana yadda mahara ke bude wuta a kan al'umma wadanda suka hada da yara da mata, da kuma cinna wa gidaje da dukiyoyin jama'a wuta. Harin na baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da  jihar Filato ke fuskantar rikicin kabilanci.