1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na neman zama tungar rikici

February 15, 2021

A yayin da ake ci gaba da lashe rayuka sakamakon rikicin unguwar Sasha da ke a jihar Oyo, hankula na tashi a yankin arewacin Najeriya, inda matasa ke kartar kasar kai karshen kisan 'yan uwansu da ke Kudu maso Yamma.

https://p.dw.com/p/3pNzl
Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Sannu a hankali, rikici da rashin tsaro na ta yaduwa a sasssan NajeriyaHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Sojojin kafar sada zumunta ta Twitter dai, sun mayar da hankali ga rikicin  na kasuwar Sasha da ke a jihar Oyo da ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 20, ko bayan raba sama da 5,000 da muhallinsu. Kuma ba su boye bacin ransu ba, kan abun da suke yi wa kallon kokarin kin jini na kabilar da ke dada mamaye sashen Kudu maso Yammacin kasar a halin yanzu. Tun kafin Sashan dai, da ma an kai ga korar Fulani a jihohin Oyo da Ogun da jihar Ondo, bisa hujjar taka rawa a cikin rikicin rashin tsaron da ke rikidewa ya zuwa na siyasa.

Karin Bayani: Fargabar barkewar rikicin kabilanci a Najeriya

Duk da cewar dai an yi nasarar tabbatar da zaman lafiya a yankin na Arewa da a baya ke zaman tunga ta ramuwar gayyar-gayya, har ya zuwa yanzu rayukan matasan yankin na bace. Alhaji Gambo Gujungu dai na zaman shugaban kungiyar matasan arewacin Tarayyar Najeriya, ya kuma ce suna shirin tona asirin masu ruwa da tsaki a tayar da rikicin da ke ta yaduwa a sassan na Kudu.
Ana dai danganta rikicin da gazawar gwamnatin wajen daukar mataki a kan masu kalaman batanci irin su Sunday Obgoho da suka rikide ya zuwa jagororin al'ummar sashen na Kudu maso Yammacin kasar, suka kuma ja ragamar shirin na kare kabilun Arewa  ta hanyar fakewa da batun rashin tsaro. Abun kuma da a cewar Alhaji Tanko Yakasai da ke zaman daya a cikin dattawan arewacin kasar, ke barazanar dora kasar bisa hanyar zama Ruwanda ta biyu.

Cartoon Nomadenkrise Nigeria
Zargin makiyaya da ta'azzara al'amuran rashin tsaro a NajeriyaHoto: Abdulkareem Baba Aminu/DW

Karin Bayani:Fulani makiyaya a Najeriya na cikin fargaba

A wannan Litinin din dai, manyan jagororin tsaron kasar sun kaddamar da wata tattaunawa a daukacin sassan kasar guda shida da nufin kwantar da hankali da kila neman shawara ta matakan dauka domin kare rikicin. To sai dai kuma a fadar Kabiru Adamu da ke zaman masanin tsaron kasar, ko bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da harkokin al'umma, gwamnatin kasar na da bukatar kallon rawar kafafen yada labarai na kasar da ke mayar da hankali wajen yada yawan kyama da kabilanci cikin kasar maimakon na sulhu a halin yanzu. 'Yan mulkin na Abuja dai na a tsakanin taunin tsakuwa da nufin ceto Najeriyar daga fadawa rikicin kabilanci da kuma kyale kasar komawa tungar rikici ta nahiyar Afirka.