1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun halaka a Plateau

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 18, 2023

Adadin wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin manoma da makiyaya a jihar Plateau da ke yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya na karuwa.

https://p.dw.com/p/4RXqI
Najeriya | Sojoji | Plateau | Rikici
Jihar Plateau na daya daga cikin jihohin da ke fama da rikici a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Rahotanni sun nunar da cewa kawo yanzu sama mutane 80 ne aka tabbatar sun halaka sakamakon rikicin, biyo bayan wani hari da aka kai a gundumar Mangu. Shugaban karamar hukumar Daput Minister Daniel da ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wasu mutanen da dama sun jikkata ba tare da ya bayyana adadinsu ba. Haka kuma ya tabbatar da cewa an lalata gidaje masu yawa, inda a yanzu haka mutane da dama sun rasa muhallansu. Ita ma Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar SEMA, ta tabbatar da afkuwar lamarin tare da cewa a yanzu haka dubban mutane sun warwatsu a kan tituna sakamakon rikicin. Dama dai jihar ta Plateau, ta kwashe tsawon shekaru tana fama da rikicin addini da na kabilanci.