1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: NLC ta dakatar da yajin aiki na wucin gadi

Uwais Abubakar Idris
June 4, 2024

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya sun sanar da dakatar da yajin aikin na kwana bakwai bayan cimma yarjejeniniya da gwamnatin tarayya a kan karin albashi mafi kankanta da kungiyar ta nema.

https://p.dw.com/p/4gdhW
Nigeria Protest NLC Abuja
Hoto: Uwais/DW

An cimma wannan yarjejeniya ce bayan tattaunawa a tsakanin wakilan kungiyar kwadagon Najeriyar karkashin jagorancin manyan kungiyoyin biyu na NLC da TUC a kan wannan batu na karin albashi mafi kankanta da ya gurgunta daukacin al'amura a Najeriyar.

Gwamnatin ta amince za ta biya yayan kungiyar kwadagon alabashi mafi kankanta da ya zarta Naira dubu 60, kuma za'a ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.

Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da NLC kan yajin aiki

'Yan kungiyar kwadago a Najeriya
'Yan kungiyar kwadago a NajeriyaHoto: DW

Sakataren gwamnatin Najeriya George Akume da ya jagoranci jami'an gwamnati a wajen tattaunawar ya bayyana abubuwan da suka cimma da ‘yan kwadagon na Najeriya.

‘'Yace bayan kwashe lokaci da dukkan bangarorin an cima wannan yarjejeniyar, shugaban Najeriya ya amince zai biya albashi mafi kankanata da ya zarta Naira dubu 60 ga ma'aikatan Najeriya, kuma wannan kwamitin zai ci gaba da taro a kowace rana na tsawon mako guda domin cimma yarjejeniya a kan albashi mafi kankanta, kungiyoyin kwadago za su zauna domin amincewa da wannan'

Karin Bayani: Najeriya: NLC ta ci tuwon fashi a kan zanga-zanga

'Yan kungiyar kwadago a Najeriya
'Yan kungiyar kwadago a NajeriyaHoto: dapd

Yajin aiki dai ya gurgunta al'amura a Najeriyar domin kusan komai ya tsaya cik. Kwararru a fanin tattalin arziki suna nuna damuwa a kan dumbin asarar da kasa da ma alummarta ke yi a dalilin yajin aiki musamman irin wannan da ya tilasata rufe bankuna. 

Janye yajin aikin dai ya samar da sa'ida ga ‘yan Najeriya domin tuni bankuna suka bude, harkokin kasuwanci suka fara dawowa dai dai tare da maido da wutar lantarki da ‘yan kwadago suka kaste da ya jefa kasar cikin duhu abin da ya sanya cikin hanzari gwamnatin ta saurare su.