1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta cimma yarjejeniya da NLC kan yajin aiki

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 4, 2024

Gwamnatin ta amince da biyan sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin albashi, a yayin da za a ci gaba da tattaunawa a kan wannan lamari

https://p.dw.com/p/4gc0M
Hoto: Uwais/DW

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta cimma yarjejeniya da kungiyar kwadagon kasar NLC a kan yajin aikin gama-gari da suke yi game da neman karin albashin ma'aikata.

Karin bayani:Kungiyar kwadago ta NLC ta fara yajin aiki a Najeriya

Gwamnatin ta amince da biyan sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin albashi, a yayin da za a ci gaba da tattaunawa a kan wannan lamari.

Karin bayani:Kungiyar NLC a Najeriya ta jingine yajin aiki

Kungiyar kwadagon za ta yi taron kwamitin gudanarwarta domin sanar da wannan ci gaba da aka samu, kafin ta sanar da janye yajin aikin.

Yajin aikin ya sanya al'amura sun tsaya cik a Najeriya, inda har zuwa wannan lokaci babu wutar lantarki, kuma zirga-zirgar jiragen sama ta tsaya, haka zalika bankuna na rufe.