1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ina makomar yajin aiki a Najeriya?

June 6, 2023

Kasa da sa'o'i 24 da shiga wani yajin aiki na sai baba ta gani a Najeriya, kungiyoyin kwadago sun dakatar da yajin aikin da ke shirin zama zakaran gwajin dafi ga makomar sabuwar gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/4SFuq
Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Yajin Aiki
Takaddamar sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kungiyar kwadagoHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

A lokaci kankane ne dai suka dau zafin da ke kama da dakin gasa burodi, haka kuma ba su ja lokaci ba wajen komawa iskar kaka a bangaren kungiyoyin kwadagon Tarayyar Najeiryar da ke fadin sun janye yajin aiki. Kungiyar NLC da 'yar uwarta TUC dai, sun fake da hukuncin wata kotun Abuja wajen ayyana janye yajin aikin da suka shirya shiga. Maimakon neman mayar da tallafin dai, wata ganawa a tsakanin 'yan kwadagon da wakilain gwamnatin tarayyata mayar da hankali wajen sanya ma'aikata cin gajiyar wasu tsare-tsare na rage radadin tallafin.

Karin Bayani: Kungiyar NLC na shirin shiga yajin aiki na gargadi

Tsare-tsaren kuma da ko bayan karin albashi, suka hada da sanya ma'aikatan kasar a kan gaba wajen rabon dalar Amurka miliyan 800 da Abujar ta ce za ta kashe a kokarin sanyaya wahalar zare tallafin. Ko bayan nan dai 'yan kwadagon na NLC da TUC neman a farfado da tsarin iskar gas da nufin maye gurbin man fetur, a matsayin  makamashin zirga-zirga a kasar. Ana dai kallon sabon matakin da kokarin rushe fatan miliyoyin 'yan kasar da ma makwabtan da ke dogaro da su cikin yajin daya zama al'ada tsawon lokaci. Kokarin karshe na tilasawa gwamnatin sauyin matsayi dai, ya faru shekaru 12 da suka gabta a karkashi na tsohuwar gwamnatin Goodluck Ebele Jonathan.

Najeriya | NLC | Abuja | Zanga-zanga
Barazanar yajin aiki ba bakon abu ba ne ga kungiyar kwadagon NajeriyaHoto: Uwais/DW

Kuma ko a wancan lokacin a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan siya da batun mulki a kasar, masu adawa na lokacin ba 'yan kwadagon ba ne suka iya kai wa ya zuwa tabbatar da kyale tallafin. Ci da gumin talakawa ko kuma neman dora kasa kan hanya ta ci-gaba dai, bukatun 'yan kwadagon kasar a fadar Joseph Ajaero shugaban kungiyar NLC, na da babban burin taimakawa daukacin 'yan kasar ba wai 'yan kwadagon kadai ba. Kokairn tafawa gwamnati ko kuma hanyar kaucewa rikici da 'yan kwadago dai, janye yajin aikin na zaman babban sauki ga masu mulkin na Abuja da ke shirin daidaita zama bisa mulki amma a cikin halin rudu.

Karin Bayani: Najeriya: Yajin aikin ma'aikata ya tsayar da al'amura.

Da kyar da jibin goshi ne dai, tsohuwar gwamnatin ta Jonathan ta ceto kanta sakamakon rikicin man da ya nemi jefa ta cikin matsalla babba. To sai dai kuma a fadar Barrister Buhari Yusuf da ke zaman  lauyan mai zaman kansa a Abuja, tsoron dauri na zaman na kan gaba wajen dakatar da barazanar yajin aikin da ma sauyin taku na 'yan kwadagon da kotu ta yanke hukuncin a kansu. Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba ga kungiyar kwadagon da ke fuskantar suka da kila ma zargin karbe na goro, a cikin rudanin zare tallafin.