1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Kirga asara bayan ibtila'in ambaliyar ruwa

Ramatu Garba Baba
July 22, 2021

Munmunar ambaliyar ruwan da ta afku a Jamus ta haddasa asarar sama da dalar Amirka biliyan biyu. Wannan shi ne karon farko da kasar ke fuskantar ibtila'i irin wannan.

https://p.dw.com/p/3xq8O
Deutschland | Flutkatastrophe NRW - Bundeswehrfahrzeuge in Erftstadt
Hoto: David Young/dpa/picture alliance

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ruwaito cewa, bala'in ambaliyar ruwan da ta afku a Jamus ta haddasa asarar sama da dalar Amirka biliyan biyu. Wata majiyar gwamnati ce ta tabbatar da hakan, biyo bayan ambaliyar da ta afku a yammacin kasar a makon jiya.

Gwamnatin Jamus ta ware akalla euro miliyan 200 daga baitul malinta dan tallafawa wadanda matsalar ambaliyar ta shafa, a yayin da hukumomin yankunan da matsalar ta fi kamari, za su samar da tallafin gaggawa na euro miliyan 400 ga jama'a.

A yayin da ake nazari kan darussan da aka koya daga ibtila'in ambaliyar ruwa, Jamusawa na tafka muhawara hasashen na'urori da manhajoji yin gargadi ga irin ibtila'in gabanin aukuwarsa. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, tayi kira domin daukar matakan gaggawa a kan yaki da sauyin yanayi.