1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a bada agaji ga mutanen da ambaliya ta shafa

Binta Aliyu Zurmi
July 15, 2021

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkwarin taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna a kasar.

https://p.dw.com/p/3wXza
Unwetter in Schuld
Hoto: Wolfgang Rattay/REUTERS

A yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan sama da Jamus ta fuskanta ya haura zuwa sama da 40, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wacce yanzu haka take ziyarar aiki a Amirka ta nuna alhininta game da wannan iftila'in tare da mika sakon jaje ga wadanda abin ya shafa.

Merkel ta yi alkawarin daukar matakin gagawa ga wanda suke kwance a asibiti domin ganin an ceto rayukansu, haka zalika ta ce za a ba su duk gudumawar da suke bukata gami da daukan matakin kare aukuwar hakan a nan gaba.

Wannan dai shi ne karon farko da yankin yammacin Jamus din ke fuskantar irin wannan mumunar ambaliya da ta yi sanadin rayukan mutane da rushe gidaje da ma lalata dukiyoyi.