1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Muhawara kan ibtila'in ambaliya

Usman Shehu Usman LMJ/RGB
July 21, 2021

A yayin da ake nazari kan darussan da aka koya daga ibtila'in ambaliyar ruwa, Jamusawa na tafka muhawara hasashen na'urori da manhajoji yin gargadi ga irin ibtila'in gabanin aukuwarsa.

https://p.dw.com/p/3xnP5
Wetterradar des Forschungszentrums Jülich am Standort Sophienhöhe
Hoto: FZ Jülich/Helmholtz-Institut

Ambaliyar ta zo wa mutane da yawa a cikin yanayi na ba zata a kasar ta Jamus da za a iya cewa, kusan ana iya kai dauki ga kowacce irin barazana. Hukumomin da lamarin ya shafa suna iya kokarinsu, to amma babu wanda ya yi tunanin afkuwar bala'in na ambaliyar ruwan da ta yi mummanar barna kamar wanda ya faru, don haka akwai Jamusawa da yawa, da ba su ma taba ganin ruwa na malala koda kan titi balle ace mummunar ambaliya da ta yi awun gaba da gidaje da motoci. 

Deutschland Hochwasser Bundeskanzlerin Angela Merkel in Bad Münstereifel
Merkel ta bayyana kaduwa kan ibtila'inHoto: Wolfgang Rattay/AFP/Getty Images

Na'urar yin gargadi ta yi kara, amma cikin karamin lokaci. Wasu da ke da manhajar a wayoyinsu, sun iya samun gargadin cewa duk wanda ke kusa da gabar ruwa da bai gaza nisan mita 50 ba, to ya fice daga gidansa. Kerstin Laubmann, wata malamar addinin Kirista da tayi karin bayani: "Mutanen ba su san ma yadda za su tinkari lamarin ba a lokacin. Kwatsam sai suka samu kansu cikin yanayin. Suna ta tattara kayayyakin daki, suna ta daukar duk abin da za su iya kawar da shi ga fadawa ambaliyar. Hakan wani mummunan yanayi ne. Suna ta kururuwa kawai."

Karin Bayani: Ambaliyar ruwa ta tagaiyara mutane a Jamus
Yanzu da ake ta tafka mahawara a kasar ta Jamus, shin me ya hana na'urori da manhajojin gargadi yin aiki, wanda da ya taimaka cikin lokaci, mazauna a gabar ruwa da sun iya tattara kayayyakinsu. Amma a cewar Michael Kopitzara, mamba a rundunar kawo agajin gaggawa, wannan mataki ne da ya kamata ya fito daga hukumomi a sama, babu yadda za a yi 'yan kwana-kwana da masu ayyukan gaggawa su iya daukar irin wannan mataki cikin karamin lokaci. Yayi karin bayani da cewa, "Hakika da mutum ya zama cikin shiri kuma da an dauki matakan cikin lokaci. Ko da kuwa idan ambaliyar ba ta faru ba, amma dai mutum na shirye. To amma wa ke da karfin zuciyar fadin hakan? domin da mutane daga daruruwan gidaje ne za a nemawa mafaka cikin 'yan sa'o'i"

An shiga aikin tsaftace muhalli
An shiga aikin tsaftace muhalliHoto: Getty Images

Ambaliyar ta kasance wa hukumomin kasar Jamus da sauran kungiyoyin ayyukan agaji a matsayin wani babban darasi, na kasancewar cikin shirin ko-ta-kwana, ko da kuwa irin wannan ibtala'i bai faru ba. Kuma ga mazauna a gabar ruwa da sunan gidajen masu hali da ke son shakatawa, akwai matukar jan kunne na so kwana da cewa, ba kullum ba ne ake kwana da ido biyu a rufe, don haka sai sun dauki kwararan matakan kariya.