1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta kashe mutane a Jamus

Abdul-raheem Hassan
July 15, 2021

An tabbatar da mutuwar mutane da bacewar wasu da dama, bayan ruftawar gidaje shida sakamakon ambaliyar ruwan sama mai karfi da ya dauki lokaci mai tsawo ana yi.

https://p.dw.com/p/3wV9V
Deutschland | Unwetter in Nordrhein-Westfalen
Hoto: Gianni Gattus/TNN/dpa/picture alliance

Rahotanni sun tabbatar da samun tsaikon ababen hawa a wasu yankunan kasar sakamakon ruwan saman, matakin da ya shafi wasu harkokin yau da kullum, wasu da dama sun yi asara mai yawa.

Hukumomi sun ce akwai karin wasu gidaje 25 da ke fuskantar barazanar ruftawa a gundumar Schuld bei Adenau, an tura jami'an agaji domin zama cikin shirin ko ta kwana yayin da aka fara kwashe wasu jama'a a yankuna mafi  hatsari.