1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Muhawara kan kalaman shugaban Najeriya

June 18, 2024

Bayan shugaban Najeriya ya bukaci sadaukarwa daga 'yan kasar sakamakon tsadar rayuwa, muhawara ta barke cikin kasar bisa batun na sadaukarwar a cikin wanaka ta dukiya a bangaren 'yan mulki.

https://p.dw.com/p/4hD2l
Manyan jami'an gwamnatin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da majalisar zastarwaHoto: Ubale Musa/DW

 

Batun na sadaukarwa dai daga duk alamu na nufin abubuwa daban-daban ga 'yan kasar da ke masa kallo da idanu daban-daban a Najeriya inda muhawara ta yi nisa bisa rayuwar masu mulkin kasar. Shugaba Bola Tinubu dai ya shaida wa 'yan kasar batun na sadaukarwa na zaman wajibi kan hanyar sake ginin kasar da ke cikin baki a halin yanzu. To sai dai kuma ya fuskanci martani mai zafi cikin gida na adawa dama ragowar jama‘ar gari da ke fadin ba hujja.

Karin Bayani: Ranar dimukuradiyya cikin kunci a Najeriya

Batun na sadaukarwa da ke zuwa a lokacin da majalisar kasar take fadin shugaban da mataimakinsa na bukatar sabbabi na jiragen hawa guda biyu dai, ta bata rai na da dama da ke mata kallon rayuwa iri guda biyu a tsakanin masu mulkin kasar da talakawan da ke tunanin gyara. Ba batun na sadaukarwa a fadar Peter Obi da ke zaman dan takara na jami‘iyar Labour a bangaren shugaban kasar da ke tunanin jirgi cikin kasar da ke fadin akwai alamun yunwa.

Masu sayar da abinci a Najeriya
Masu sayar da abinci a NajeriyaHoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

Rayuwa guda biyu ko kuma zahirin bukatar mulki dai, a baya dai shugaba Tinubu ya kai ga jirgi na haya da nufin kaucewa hadari sakamakon lalacewar jirgin. Kuma akwai batun siyasa cikin ikirarin jirgin na zaman alamun dadi a cikin matsin rayuwa a fadar Bishir Dauda da ke zaman wani jigo a cikin jam'iyyar APC da ke da mulki a kasar.

Siyasa cikin batun yin mulki, ko kuma neman sauyi ga kasa, ikirarin neman sauyin a banagren na Tinubu dai a tunanin Faruk BB  Faruk dake sharhi cikin batun yin mulki, ya saba da rayuwa da ke a tsakanin 'yan mulkin Najeriya a halin yanzu. Cikin batun na sadaukarwa ne dai masu mulkin tarayyar Najeriyar su kai tsaiwa irin ta gwamin jaki cikin mafi karancin albashi, cikin kasar da hauhawa ta farashi na ababe na more rayuwa suke kara sama, kuma samu na 'yan kasar ke raguwa.