1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shekaru 25 da mulkin Dimukuradiyya

Uwais Abubakar Idris
May 29, 2024

Dubban yan kungiyoyin cigaban dimukurdiyya da matasa sun gudanar da tataki don murnar cikar Najeriya shekaru 25 da mulkin dimukurdiyya a Najeriya ba tare da katsewa ba

https://p.dw.com/p/4gQw1
Hadakar kungiyoyin farar hula na Najeriiya
Hadakar kungiyoyin farar hula na NajeriiyaHoto: Uwais/DW

Rana ce dai mai muhimmancin gaske ga ‘yan Najeriya da ya sanya su biki har da taka rawa domin wannan ne karon farko da yan kasar suka kwashe shekaru 25 suna zabe bisa tafarkin dimukurdiyya, halin da a shekarun baya basu same shi ba saboda katsalandan na sojoji a mulki. 

Tarihin Najeriya ya kasance wanda yake cike da katsewar mulkin dimukurdiyya sanin cewa shekaru shida da samun ‘yanci ne aka fara samun tangarda abinda kwarraru ke bayyana cewa ya mayar da hannun agogo baya a fanin mulkin farar hula. Dagewar da kasar ta yi na kaiwa ga wannan matsayi da ya daga darajar kasar muhimmi ne. 

To sai dai duk da ci gaban da aka samu na dorewar mulkin dimukurdiyya a wadannan shekaru da ma ikon fada a ji da kafa kungiyoyi da jamiyyun siyasu, yan Najeriyar sun ga tasku a wadannan shekaru musamman rigiungimun da kasar ta samu kanata a ciki kama daga matsalar rashin tsaro ya zuwa koma bayan tattalin arziki. 

Wannan tattaki na bikin cika shekaru 25 da mulkin dimukurdiyya da aka gudanar a Abuja an gudanar da imakamancinsa a daukacin jihohin Najeriya karkashin gamaiyyar kungiyoyin bunkasa dimukurdiyya ta Najeriya da ta tattara kungiyoyin fararar hula da suka yi fafutuka wajen tabbatar da dorewar mulkin farar hula.