1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daure masu saba dokar corona a Najeriya

January 28, 2021

Daga yanzu duk wanda ya saba wa dokokin kiyaye yaduwar annobar cutar COVID-19 a Najeriya, zai iya fuskantar hukuncin dauri a gidan kaso.

https://p.dw.com/p/3oWhW
Nigeria Lagos | Coronavirus | Temperaturmessung
Kin bin ka'idoji da matakan kariya kan corona, ka iya sa mutum zaman gidan yariHoto: DW/F. Facsar

Wannan matakin dai ya biyo bayan sanya hannu kan wata doka da aka fito da ita don karfafa yaki da cutar, wacce ta ke kara yaduwa a kasar. Hukuncin wanda duk aka samu ya karya dokar ko ka'idojin yaki da yaduwar cutar COVID-19 din a Najeriya wanda ba za a bata lokacin wajen yanke wa ba, shi ne zaman wata shida a gidan yari ko gidan gyara halinka ko zabin tara ko kuma a hada duka biyun. Bayyanar dokar a wannan lokacin dai, bai rasa nasaba da yadda cutar COVID-19 wacce ta sake dawowa a karo na biyu da karfi, ke kara yaduwa a sassan Najeriya kamar wutar daji ba.

Karin Bayani: Matsalar kin zuwa gwajin corona a Najeriya

Hukumomi sun lura da cewa kullum alkaluman sababbin masu kamuwa da cutar na karuwa, abin da suke alakantawa da kunnen kashi da ake zargin 'yan kasa na da shi wajen bin dokoki ko ka'odijin da hukumomin su ka zayyana, domin kare kai daga kamuwa da cutar. Samar da wannan doka kan corona dai, na nufin cewa daga yanzu, duk wanda aka samu yana dauke da cutar ya nemi kin zama a wurin da hukumomi suka ware domin killace shi ko kuma rashin bayar da tazara a wuraren haduwar jama'a gami da rashin amfani da takunkumin fuska wato "Face Mask,” ko kin wanke hannu ko amfani da sinadarin tsabtace hannu, to dokar za ta yi aiki a kansa.
A cewar masana harkokin kiwon lafiya masu yaki da yaduwar wannan cuta kamar Sama'ila Idris Hinna jami'in lafiya a asibitin koyarwa na tarayya da ke Gombe a Najeriyar, dokar kan COVID-19 ta zo a kan lokaci. Tuni dai al'ummar kasar suka fara mayar da martanin kan wannan matki, inda wasu ke goyon baya wasu kuma ke ganin za a kara takurawa talakawa ne bisa matsatsin da suke ciki na yunwa da rashin tsaro.

Karikatur Die 2. Corona-Welle in Nigeria
Coronavirus ta sake dawo wa a karo na biyu a kasashe da dama ciki har da Najeriya

Karin Bayani: Rudani kan shirin samar da rigakafin corona a Najeriya

Malama A'isha Haruna wacce aka fi sani da Gimbiya tana cikin masu maraba da wannan doka, kuma a fahimtarta an yi ta ne domin ceto rayuwar al'umma. Sai dai Auwal Hassan na da bambancin ra'ayi, inda ya ke ganin ba abin da wannan doka za ta yi sai kara jefa talakawan Najeriyar cikin ukuba. Shi kuma Khalid Idris Doya wani mai fashin baki kan harkokin yau da kulkum, neman gwamnatin ya yi da ta fara gwada dokar a kan manyan jami'anta da 'yan siyasa, yana mai cewa ta hakane za a tabbatar da dokar za ta yi tasirin da ake nema. Akwai kuma da dama da ke da ra'ayin cewa, koda an kafa doka akwai bukatar gwamnati ta karfafa ayyukan fadakar da al'umma a kan wannan cuta, ganin har yanzu akwai wadanda ke ganin ta a matsayin wata makarkashiya da gwamnatocin ke son fakewa da ita su biyan wasu bukatunsu.