1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Dokar Corona ta leko ta koma

Nasir Salisu Zango GAT
June 2, 2020

A Najeriya Kanawa na mayar da martani kan matakin gwamnatin Kano na ci gaba da aiki da dokar kulle da takaita zirga-zirga ta Corona duk da matakin gwamnatin tarayya na dage dokar a jihar.

https://p.dw.com/p/3d8wV
Nigeria Lagos | Coronavirus | Straßenverkäufer
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Murna ce ta koma ciki ga galiban alummar jihar Kano musamman ma 'yan kasuwa da ke murnar sanarwar da gwamnatin tarayya ta bayar a yammacin jiya Litinin inda ta ce ta sassauta dokar kulle a kano tare da sanya dokar takaita zirga zirga daga karfe shida na safe zuwa takwas na dare.

To amma daga bisani cikin dare kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Comrade Muhammad Garba ya fitar da sanarwar cewa gwamnatin Kano ta yi wa waccan sanarwa ta gwamnatin tarayya kwaskwarima, inda ta ba da sanarwar bude kasuwanni amma kuma dokar kulle tana nan daram,in ban da ranaikun Lahadi da Laraba da Juma'a da aka aminta a fito a ci kasuwa a koma Sharfa Kantin Kwari dan kasuwa ne a kasuwar sabon garin Kano ya ce waannan sassauci na umarcin bude kasuwanni tamkar tufka da warwara ce domin dama 'yan kasuwa sun galabaita kuma hakan zai iya jefa su cikin rudani.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Hoto: Salihi Tanko Yakasai

Dalilin sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar da yamma da kuma labarii da aka samu na fitowar sanarwar gwamnatin jiha wanda sai a cikin dare ya fito ya sa mutane cikin dimuwa, suka fito domin neman abinci har ma kuma sun gamu da halin ba sani ba sabo na jamian tsaro da aka sanya gadin hanyoyi ,harma a zantarwarmu dasu suka ce ba su san gwamnatin jiha ta bayar da sanarwar da ta warware ta gwamnatin tarayya ba

Masana masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum irin su Ambasada Muktar Gashash,ya ce galiban mutane sai sun fita za su sami abinci dan haka ya ke shawartar gwamnatin jiha ta sassauta.
Bashir Ahmed shi ne hadimin shugaban kasa a fannin kafafen sadarwa na zamani ya ce,dama batun yadda za a yi da kasuwanni yana hannun gwamnatin jihohi.

Grenze zwischen Lagos und Ogun - Polizeikontrolle
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Zuwa safiyar wannan Talata dai galiban mutane 'yan rabbana ka wadata mu na kuka bisa yadda suka ce zaman gidan ya isa,domin a fahimtarsu hadarin yunwa ya fi na Corona dan haka suke neman sassauci.