1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Talakawa a Kaduna sun damu saboda tsadar gidajen haya

January 12, 2021

A Kaduna da ke arewacin Najeriya, tsadar gidajen haya a yanayi na koma bayan tattalin arziki da yaduwar annobar corona na janyo matsalolin da ke shafar masu zama a gidajen haya.

https://p.dw.com/p/3npZC
Nigeria Region Bauchi grünes Haus
Hoto: DW/A. Hazzad

Tsadar gidajen haya a yanayi na matsin tattalin arziki da yaduwar cutar corona na ci gaba da janyo matsalolin da ke shafar masu zama a gidajen haya, lamarin da ya sanya kungiyoyin kare hakkin bill Adama da malaman addinai yin kira gami da bukatar rage kudin gidajen haya donn saukaka wa talakawan kasa.

Malam Umar Mai-barno daya ne daga cikin fitattun dillalan da ke bayar da gidajen haya a Kaduna ya bayyana cewa tsadar gidajen haya a cikin wannan yanayi na matsin tattalin arziki da cutar corona ya sanya mazauna gidajen haya cikin birane da karkara gaza biyan kudaden da ya kamata su biya na zama cikin gidan haya.

Ya ce wannan al'amari ya sanya da damar gaske daga cikin masu ire-iren wadannan gidajen haya fara yunkurin sayar da wasu gidaje a farashi mai sauki da ma karya farashin wasu daga cikin su domin rashin kudi da ke damun mutane a irin wannan lokaci na annobar Covid-19.

Babu shakka dai sake fadawar Najeriya cikin matsalar karayar tattalin arziki na ci gaba da zama wani babban kalubale musamman ga bangaren talakawan kasa, saboda haka ne ma wasu masu gidajen ke tausayawa, suna yi wa masu haya sassauci.

Gami da wannan matsala tuni malaman addinai tare da masu kare hakkin bil Adama suka fara fitowa ta kafafen watsa labarai don fargar da al'umma a kan hatsarin amfani da wannan damar wajen cutar da bayin Allah.