1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shekaru 64 da samun 'yanci

October 1, 2024

A cikin yanayin rudu da kila ma bambanci na tunani, masu mulkin Najeriya na bikin cika shekaru 64 na 'yancin kan kasar.

https://p.dw.com/p/4lIgL
Najeriya | Yanci | Shekaru 64 | Turawa | Mulkin Mallaka | Birtaniya | Tsadar Rayuwa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Presidencial Villa Abuja

An dai busa begila an kuma yi faretin al'ada, amma duk a cikin fadar gwamnatin Najeriya inda shugabannin kasar da ma muhimman baki suka hallara domin murnar shekaru 64 d samun 'yancin kan kasar daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Bikin da ya gudana a farfajiyar fadar gwamnatin kasar dai, na zuwa ne a cikin yanayin matsin tattalin arziki da ma rashin tsaro da kasar ke fama. Tun da sanyin safiya shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya dauki lokaci yana ta jawabi, a kan batutuwa da daman gaske. Kuma kama daga wata sabuwar nasara cikin batun tsaron ya zuwa kokarin rage radadin rashin tsaro dai, Tinubun ya ce zai yi duk abun da ke akwai da nufin sauya makomar kasar da ya ce ya gada a cikin yanayi maras kyau.

Najeriya | Yanci | Shekaru 64 | Turawa | Mulkin Mallaka | Birtaniya | Tsadar Rayuwa
Faretin bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin cin gashin kan NajeriyaHoto: Presidencial Villa Abuja

Tinubun dai ya ce sauyin tattalin arzikin na samun nasara, haka shi ma batun rashin tsaron da ke nuna alamun haske: "Babban burinmu shi ne mu kai karshen duk wata barazana daga Boko Haram da satar al'umma da ma duk wata barazana ta rashin tsaro. A cikin shekara guda mun kashe 'yan ta'addar da adadinsu ya wuce na ko yaushe a cikin tarihin kasar, a kiddidgarmu ta karshe mun kashe sama da 300 a Arewa maso Yamma da Arew maso Gabas da ragowar sassan kasar. Mun sake dawo da zaman lafiya ga daruruwan garuruwa a Arewa, sannan kuma dubban al'ummarmu sun sake komawa zuwa gida. Aikin bai kare ba kuma da zarar mun samu karin ceto al'umma, to manomanmu za su koma gona kana farashin abinci zai ragu. Nai muku alkawarin wannan, kuma ba zan gajiya ba."

Tsaro: Gwamnan Katsina ya magantu

Koma ya zuwa ina Abujar ke shirin ta kai, nasarar dai a fadar Mohammed Badaru Abubakar da ke zaman ministan tsaron kasar na da ruwa da tsaki da dabarun 'yan mulkin. Sai dai a yayin da masu mulkin ke fadin sun yi nasara a lokaci kankane, zamani na Tinubun na zaman na auren zobe a tsakanin majalisun kasar guda biyu da bangaren zartarwar da ke rawa tana yin juyi. Ana ma dai zargin majalisun da komawa zuwa amshin shata na banagren zartarwar, a karkashin wani tsarin da ya kalli 'yan majalisar biya na bukatar bangaren zartarwar ko yaushe. Sai dai 'yan majalisar, a fadar mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Barau Jibrin ba sa tunanin rikicin da babu fa'ida ga al'umma. Nasarar cikin batu na hadin kai ko kuma hada kai domin cutar talaka dai, Najeriyar na shirin dorawa a cikin doguwar tafiyar a cikin yanayin da ba shi da tabbas cikin batu na tattalin arziki da siyasa.