1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zanga-zanga na neman zama rudani

Uwais Abubakar Idris LMJ
August 1, 2024

Ana can ana dauki ba dadi tsakain jami'an tsaro da masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, bayan da matasan da suka fito sun bijirewa umurnin jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/4j18i
Najeriya | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu | Matasa | Zanga-Zanga | Tsadar Rayuwa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Masu zanga-zangar da suka bazama kan tituna, sun bi bababban titin da ya taso daga kofar Abuja zuwa tsakaiyar birnin tare da rera wakokin bayyana halin tsadar rayuwa. A cewarsu, hakan ce ta sanya suka dage kan lallai sai sun nunawa gwamnatin Najeriyar halin da ake ciki. An yi ta canza wurin da aka shirya gudanar da zanga-zangar a birnin na Abuja, kafin su hallara a filin wasa na kasa. A can ma sun tirje cewa ba za su shiga ciki ba duk da matsawar da kwamshinan 'yan sandan Abujan ya yi, abin da ya janyo tashin hayaniya. 'Yan sanda sun ta harba barkonon tsohuwa, domin tarwatsa masu zanga-zangar a lokacin da suka yi kokarin kai wa dandalin.

Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Zanga-zangar dai ta tilasata harkoki sun tsaya cik a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar tamkar ranar hutu, domin daukacin ma'aikatan gwamnati sun kauracewa ofisoshinsu an kuma rufe bankuna kana motocin haya ma sun tsaya cik in ban da jami'an tsaro da ake gani a birnin. Duk da umurnin da kotu ta bayar da na 'yan sanda da suka nemi masu zanga-zangar su tsaya wuri guda sai da suka bi titunan Abuja da tattaki na tsawon kilomita bakwai zuwa tsakiyar birnin Abujan, inda suka ci gaba da artabu. Mikail Idris na cikin masu zanga-zangar. Tsawon kwanaki 10 masu zanga-zangar suka tsara za su kwashe suna gudanar da ita, inda a ranar farko ta gurgunta daukacin harkokin rayuwa da tattalin arziki a birnin.