1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yancin kai da tarin kalubale

Uwais Abubakar Idris
October 1, 2023

Najeriya ta cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai a daidai lokacin da kasar ke kara fuskantar kalubale iri dabam daban da ke shafar yanayin zamantakewar rayuwar alumma.

https://p.dw.com/p/4X1cC
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Shekaru 63 ga rayuwar kowace kasa a matsayinta na mai ‘yanci bayan kubuta daga mulkin mallaka lokaci ne mai tsawo da ya kamata a ce ta samu ci gaban da alummarta za su yi alfahari da ita. Najeriyar da ta samun ‘yancin kanta daga hannun turawan Birtaniya a ranar 1 ga watan Octoban 1960 abin da ya nuna cika shekaru 63 cur a matsayin ‘yantacciyar kasa. To sai dai shekarun cike suke da kalubale, matsaloli da ma koma baya, a yanayi na rawar ‘yan mata in an yi gaba a koma baya. 

Video Afrika Odunayo Oreyeni Wahlen Nigeria
Hoto: DW

Najeriyar dai ta cika shekaru 63 da samun ‘yancin kan ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsaloli na koma bayan tattalin arziki, rashin aikin yi, mummunan rashin tsaro da ya shafi kusan daukacin sassanta, ga rashin aikin yi baya ga rashin wadataccen abinci.

Karin Bayani: kalubalen Najeriya bayan shekaru 61 da 'yancin kai

Ba kamar shekarun baya ba da akan yi gagarumin biki har da gayyatar wasu shugabanin kasashen duniya, Najeriyar ta yi bikin ne a yanayi na ba yabo ba fallasa saboda matsalolin da alumma ke fuskanta. Sanata George Akume shine saskataren gwamnatin Najeriyar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na NajeriyaHoto: APTN

‘'Yace gwamnati na sane da matsalolin tattalin arziki da ke fuskantar alummarta tun bayan cire tallafin man fetur da kuma matsalolin tattalin arzikin kasa. Amma duk da guguwar juyin mulki a yankin Afrika ‘yan Najeriya sun rungumi dimukurdiyya a matsayin tafarkin mulkin da yafi kyawu''.

Amma ya zuwa yanzu duk da wannan hali da ake ciki ko ‘yan kasar musamman matasa za su ce kwaliya ta biya kudin sabulu. 

Bisa la'akari da matsalolin da ake fuskanta a yanzu, ko mece ce mafita ga Najeriyar ganin ta cika shekaru 63 da samun ‘yanci a yanzu? 

Kodayake akwai masu ra'ayin cewar matsaloli sun lullube nasarorin da aka samu a kasar don haka ba dalilin wani biki, amma ga gwamnatin ta ce dorewar mulkin dimukurdiyya tun daga 1999 da aka sake kafa shi a kasar da ci gaba da zaman Najeriya kasa daya alumma daya abin murna ne da farin ciki.