1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko zanga-zanga za ta taimaka?

August 2, 2023

A cikin halin faduwar gaba da tsaurara tsaro, kungiyoyin kwadagon Najeriya sun shiga zanga-zangar sai baba-ta-gani kan karin farashin man da ya janyo takkadama a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/4Uh0T
Najeriya | Abuja | NLC | TUC | Kungiyoyin Kwadago | Zanga-zanga
Ba dai yanzu ne kungiyoyin kwadago suka fara yin zanga-zanga a Najeriya baHoto: Uwais/DW

Dubban 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriyar ne dai suka hau kan tituna da nufin nuna adawarsu da matakin gwamnatin kasar na zare tallafin man fetur, duk da dimbin fargaba da ma tsaurara matakan tsaro da hukumomin kasar suka yi. Duk da gargadin hukumomin kasar dai, manyan kungiyoyin NLC da na TUC sun rika rera wakokin yin tir da matakin da a cewarsu ke da babban burin jefa kasar a cikin rudani. Sun kuma ce gwamnatin kasar ta gaza cika alkawarinta na daukar matakan rage radadi, kafin ta kai ga zare tallafin. Kokari na gyara ga kasa ko kuma jefa Najeiryar cikin barazana dai, zanga-zangar na faruwa cikin halin dar-dar. Akwai dai tsoron yiwuwar rikidewar adawar 'yan kwadagon, zuwa tayar da hankalin da babu irinsa cikin kasar da ke ta kokarin sake daukar saiti.

Najeriya | Kuncin Rayuwa | Abinci
Ba dai kowa ne ke iya cin abinci sau uku a rana ba a yanzu haka a NajeriyaHoto: Atmosfair/dpa/picture alliance

Tuni dai aka fara hango barazana ta tayar da hankalin tare da wasoson abinci a rumfunan gwamnatin kasar a jihar Adamawa, sai dai kuma a fadar Ayuba Wabba da ke zaman tsohon shugaban kungiyar NLC a kasar sun yi tsarin tabbatar da komai ya tafi daidai. Koma ina zanga-zangar 'yan kwadagon take shirin zuwa akokarin cika burin gyaran lamura dai, a baya talakawan kasar sun zargi kungiyar tasu da karbe na goro a cikin sunan kare hakkin 'yan kasa. To sai dai kuma a fadar Kwamared Abbayo Nuhu da ke zaman sakataren kungiyar TUC ta manyan ma'aikatan kasar, auren zoben da ke tsakanin kungiyar kwadagon da talakawan kasar zai dore har Mahdi. Abun jira a gani dai, na zaman yadda take shirin kayawa a tsakani kungiyar da ke fadin ana ta yaudara da Abujar da ke tunanin samun haske daga zare tallafin a cikin kankanin lokaci.