1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarima bin Salman zai halarci taron G7

June 7, 2024

Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya zai bi sahun shugabannin da za su halarci taron koli na G7 da zai gudana a kasar Italiya.

https://p.dw.com/p/4gnyQ
Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya
Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya Hoto: Sergei Savostyanov/Sputnik/REUTERS

Yarima mai jiran gado na Saudiya, Mohammed Bil Salman zai bi sahun wasu shugabannin kasashe 12, da za su halarci taron koli na kasashe masu karfin arzikin masana'antu na G7 da kasar Italiya ke karbar bakunci. Gayyatar wasu shugabannin da ba kasafai ake ganin hakan ba, na daga cikin yunkurin Italiyar na kara fadada taron na G7, na manyan kasashen masu karfin tatattalin arziki a duniya.

Karin bayani: Kammala taron koli na kasashen G7

Ana kuma sa ran shugabannin kasashen Indiya da Afirka ta Kudu da Brazil da Argentina da Turkiyya da Algeria da Kenya da kuma Mauritania su halarci taron, na ranakun 13 zuwa 15 ga watan Yunin 2024. Wannan dai shi ne karon farko, da a ka  gayyaci wani shugaba daga kasar Saudiyya, da ake mata kallon mai take hakkin bil Adama zuwa taron na G7.