1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana taron kolin shugabannin kasashen G7 a Jamus

Abdullahi Tanko Bala ZMA
June 27, 2022

Shugabannin kasashen G7 masu karfin tattalin arziki na duniya na taro a Jamus. Yakin Rasha da Ukraine da matsalolin sauyin yanayi da yunwa da talauci na cikin batutuwan da za a tattauna.

https://p.dw.com/p/4DGIM
Schloss Elmau G7-Gipfel 2022 - erste Arbeitssitzung
Hoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

Taron zai gudana ne a kudancin Bavaria inda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya karbi bakuncin sauran shugabanin kungiyar ta G7 da suka hada da Faransa da Birtaniya da Italiya da Japan da Kanada da kuma Birtaniya.

'Yan sanda dubu 18 aka baza domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya tare da tabbatar da cewa babu dan zanga-zanga da za ta iya kuwa kusa da inda ake taron. Gwamnatin Jamus da ta jihar Bavaria, sun kasafta kudi dala miliyan 190 domin tsaro kawai.

Taken taron dai shi ne ci gaban da aka samu wajen samar da daidaito a duniya, kuma batun mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine da kalubalen da hakan ke haifarwa, za su mamaye jadawalin muhawara a taron.

Olaf Scholz na Jmaus, ya ce yana da muhimmanci a mayar da hankali wajen taimaka wa nahiyar Asia da Afirka da kuma kudancin Amurka. Ana sa rai a rana ta biyu na taron, shugabannin na G7 za su gana da shugabannin Indonesiya da Inda wadda ke rike da shugabancin kungiyar G20 ta kasashe masu arzikin arziki da shugaban Afrika ta Kudu da na Senegal mai rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Argentina mai rike da shugabancin kungiyar kasashen kudancin Amurka da yankin Carribean.