1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli na kasashen G7

Ramatu Garba Baba
June 30, 2022

Shugabannin kungiyar kasashe masu arziki na G7 sun kammala taronsu a Jamus, inda suka aike da sakon hadin kai bisa la'akari da halin da ake ciki na yakin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4DTmW
G7 Gipfel Elmau 2022 | Kanzler Scholz nach Abschluss-PK
Hoto: AFP

Shugabanin kasashen Birtaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan kana da Amirka, sun cimma matsayar bada goyon bayansu ga Ukraine a kokarin da suke yi na ganin an rage dogaro da makamashin Rasha, da kara matakan hukunta Moscow.

Shugaban gwamnatin Jamus kuma mai karbar bakuncin taron na yini uku da ya gudana a tsibirin Elmau da ke Bavariya Olaf Schol ya ce, kungiyar kasashen bakwai masu arziki na duniya za su ci gaba da kasancewa a bangaren Ukraine. 

Fraministan Italiya Mario Draghi ya ce kasashen na G7 sun damu matuka kan yadda sojojin Rasha ke ke kara matsowa zuwa yankin gabashin Ukraine, sai dai shugaba Volodymyr Zelenskyy na da yakinin cewar, Uukraine za ta cimma nasarar yin martani.