1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kai wa Islamiyya hari a Najeriya

November 7, 2023

'Yan bindiga a Najeriya sun bude wuta kan wata makarantar Islamiyya a arewacin kasar, inda rahotanni ke cewa sun kashe kananan yara tare da jikkatar wasu.

https://p.dw.com/p/4YWfl
Makarantar Muhammadiyya a Najeriya
Makarantar Muhammadiyya a NajeriyaHoto: DW

'Yan bidnigar bisa babura sun kai harin ne a lokacin da ake bikin Maulidi a kauyen Kusa da ke yankin gundumar Musawa, sannan kuma sun jikkata karin wasu mutanen akalla 20 bayan kisan dalibai 13.

Wani babban jami'in gundumar ta Musawa Habibu Abdulkadir, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne  maharan suka aikata wannan danyen aiki.

Jihar Katsina da wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriyar dai na fama da 'yan bindigar da kan yi garkuwa da mutane da kokane-konen garuruwa gami da kwashe dukiyoyi.

Runudnar 'yan sanda ta Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin na karshen mako.

Ko a cikin watan Disambar 2020 ma dai, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Islamiyya da suka halarsci wani bikin na Maulidi a gundumar Dandume a jihar.