1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zagayowar bikin Maulidi

Gazali Abdou Tasawa
December 11, 2018

A daren 11 washe garin 12 ga watan Rabi'ul Awal Al'ummar Musulmi suka gudanar da tarukan maulidin zagayowar shekaru 1450 da haihuwar Annabi Muhamadu a garin Makka.

https://p.dw.com/p/39rQv
Nigeria Ramadan
Hoto: picture-alliance/AA/M. Elshamy

Birnin Damagaram na jamhuriyar Nijar na daga cikin garuruwan da al'ummar Musulmi ta gudanar da wannan biki kuma, Cheik Imam malam Amadu mai wa'azi daya daga cikin jagororin Musulmi a birnin na Damagarm ya yi bayani a game da fa'idar wannan biki na tunawa da ranar haifuwar manzon rahama. Tsohon shugaban kasar Nijar Alhaji Mahaman Usman da kansa ya ja karatun littafiyar ishriniya a ranar babban daren. Dubban Musulmi ne maza da mata da yara dai suka halarci masallatai da zawiyoyin da ke shirya tarukan maulidin a birnin na Damagaram. A makobciyar kasar ta Nijar ma dai cewa da Tarayyar Najeriya Musulmi sun raya babban daren a garuruwa da dama. Birnin Bauchi na daga cikin biranen da aka gudanar da wannan biki na maulidi kuma Sheik Kabir Al-Arabi Bauchi daya daga cikin shugabannin darikar Tijjaniya a garin na Bauchi ya yi bayani a game da tarihin kafuwar bukukuwan maulidin a cikin al'ummar Musulmi.