1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikicin Twitter da gwamnati na daukar dumi

June 7, 2021

Gwamnatin Najeriya ta umarci kafafen labaran kasar da su dakatar da amafani da Twitter har sai abin da hali ya yi, a daidai lokacin da rikici a tsakaninta da kamfanin Twitter ke dada kamari.

https://p.dw.com/p/3uYQc
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Sannu a hankali rikicin tsakanin Twitter da gwamnatin Najeriya na dada kamari, haka zalika tasirinsa na kara fitowa fili a sassa dabam-daban na rayuwar al'umma a kasar. Ko bayan dakatar da harkoki Twitter a daukacin fadin tarrayar Najeriya, a wannan Litinin, gwamnatin kasar ta kuma umarci daukacin kamfanonin labaran kasar da su dakatar da amfani da Twitter a gidajen radiyo da talabijin. Duk da cewar gwamnatin Najeriya bata ambaci hukunci kan amfani da Twitter a bangaren kafafen yada labarai ba, sanarwar hukumar NBC tace rashin kishin kasa ne ci gaba da amfani da kafar ta Twitter domin neman labarai daga bangaren kafafen yada labarai na Najeriya.

Karin Bayani: Hana masu mulkin kama karya barci

Tun kafin kafafen labarai gwamnatin kasar ta yi barazanar hukunta duk wani dan Najeriya da ta samu da hannu wajen karya umarnin dakatar da amfani da Twitter ta bayar a kasar. Sama da mutane miliyan 40 ne aka kiyasata masu amfani da kafar Twitter a cikin tarrayar Najeriyar, sannan kuma ana ci gaba da kirga asarar daga ita kanta Twitter ke samu na kusan Naira Miliyan dubu 11 na kudin shiga a Najeriya ya zuwa kasar da al'ummarta ke asarar da ta kai tsakanin naira Miliyan 2000 zuwa da rabi  tun daga ranar Alhamis din makon daya shude.  Masanan tattalin arziki a Najeriya kamar Abubakar Ali na ganin rikicin dake tsakanin bangarorin biyu yafi karfin lisafin Naira da Kobo."Ya ce gwamnatin Najeriya na hasara a cikin wannan rikici haka 'yan kasa ma na hasara kamfanin Twitter kansa na tafka hasara, to amma ba kawai batun hasara ba ne, zance ne na kishin kasa domin sai in akwai Najeriya ake samun damar yin hada hadar kudi."

Karin Bayani: Kafa cibiyar Twitter a Ghana maimakon a Najeriya

Ya zuwa ranar yau dai ma'aikatar harkokin  wajen tarayyar Najeriya ta aika sammaci ga zuwa jakadun Amirka da Birtanniya  dama ragowar kasashen Turai da suka tsoma baki a cikin rikicin ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana wa kasashen ketaren da cewar dole ne kamfanin Twitter ya yi wa tarayyar Najeriya da'a  da mutunta dokokinta a gabanin duk wani mataki na sake dawo da Twitter a Najeriya. Wasu majiyoyi sun ce kamfanin ya aike da wata wasikar zuwa ga hukumomin Najeriya inda a ciki ya bayyana anniyarsa ta yin biyayya ga dokokin Najeriya.