1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Twitter ya rusfe shafuka 70,000 a Amirka

Abdul-raheem Hassan
January 12, 2021

Kamfanin twitter ya toshe shafukan 'yan kungiyar yada akida da farfagada ta QAnon bayan da suka yi kutse a zauren majalisar dokokin Amirka.

https://p.dw.com/p/3npKs
Twitter Logo
Hoto: picture-alliance/AP Images/STRMX

Kamfanin Twitter ya dauki matakin rufe shafukan 'yan kungiyar kusan 70,000 saboda kare barazanar tashin hankali da kuma rage kaifin yada mumunar akida da labaran karya.

Twitter ya ce an samu 'yan kungiyar da suka bude shafuka da dama domin ci gaba da yada manufofin Shugaban Donad Trump, ciki har da yayata cewa shi ya za ci zaben Amirka.

Kamfannonin Facebook da Twitter sun jaddada matsayarsu na tsawaita wa'adin haramta wa Shugaba Trump amfani da shafukan tun bayan dakatar da shi jim kadan bayan da magoya bayansa suka tarwatsa zaman majalisa.