1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Touadera ya sha rantsuwar mulki a wa'adi na biyu

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
March 30, 2021

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera ya sha rantsuwar fara wa'adi na biyu na mulki a Bangui babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3rNqA
Zentralafrika I Wiederwahl von Präsident Faustin Archange Touadéra
Shugaba Touadéra ya lashe zaben da ke cike da cece-kuceHoto: Nacer Talel/AA/picture alliance

Duk da cewa ya yi alkawarin daukan matakan hada kan kasa, amma kuma a daya bangaren ya haramta wa 'yan adawa barin kasar bisa dalilai na tsaro. 'Yan adawa ba su halarci bikin rantsar da Faustin Archange Touadera a birnin Bangui ba, lamarin da ke nuna irin jan aikin da ke gaban shugaban na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wajen cika burinshi na mayar da kasar tsintsiya madaurinki daya. Dama daya daga cikin manufofin da ya sa a gaba shi ne, tattaunawa da bangarorin da ke gaba da juna, domin samar da zaman lafiya a kasar. Sai dai yunkurin ya zo a daidai lokacin da aka haramta wa abokan hamayya yin balaguro zuwa kasashen waje, ciki har da madugun 'yan adawa Anicet Georges Dologuélé da Martin Ziguélé da Abdou-Karim Meckassoua tsohon kakakin majalisar dokokin kasar. Amma bayan ga cizawa da ya yi, Faustin Archange Touadera ya hura inda ya yi kira ga 'yan kasa da su ba da hadin kai a tattaunawar neman mafita da za a shirya.

Zentralafrikanische Republik - Anicet Georges Doleguele
Madugun adawa Anicet Georges DologuéléHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Karin Bayani: Takaddamar zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sai dai 'yan adawa sun yi watsi da tayin da shugaban ya yi musu na hada karfi da karfe da nufin ceto kasarsu daga mawuyacin hali da ta samu kanta a ciki. Barrista Nicolas Tiangaye wanda ke zama kakakin gamayyar jam'iyyun adawa ta COD-2020 ya bayyana dalilansu, inda ya ce Touadera ba shi da hurmin daukan wannan mataki saboda ba shi ya ci zabe ba, duk da wannanrikici da ke wakana tsakanin bangaren da ke iko da na 'yan adawa, 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suna kira ga hukumomi da su hanzarta warware matsalolin da ke addabarsu a yau da kullum, a yayin da ake jiran mafita daga kangin siyasa da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta samu kanta a ciki, daya daga cikin kalubalen fadar mulki ta Banguishi ne, shigar da shugabannin kasashen makwabta na yankin su sulhunta rikicin. Muryar shugabannin ba ta zo daya ba a kan hanyoyin da za bi wajen gudanar da tattaunawar zaman lafiya cikin nasara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.