1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran Bagui ga kasar Faransa kan tsaro

May 8, 2013

Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Nicolas Tiangaye ya yi kira ga kasar Faransa da ta taimakawa kasarsa da sojoji domin dawo da doka da oda a Bangui babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/18UeA
Hoto: DW/Leclerc

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta bukaci Faransa ta taimaka mata da sojoji domin shawo kan matsalar tabarbarwar harkokin tsaro da ta ke fama da ita a Bangui babban birnin Kasar. Firaminista Nicolas Tianguaye ne ya yi wannan sanarwa a lokacin wani taron manaima labarai da ya gudanar, inda ya nunar da cewa sai da gudunmawar sojojin ketare ne za a iya kawo karshen kwasar ganami da tsaffin 'yan tawaye na seleka ke ci gaba da yi.

Batun na tsaro na ci gaba da zama babban kalubale ga Michel Djotodia da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa bayan da ya hambarar da Francois Bozize daga karagar mulki. Mutane 20 ne dai suka rasa rayukansu a farkon watan Afrilu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a jerin tashe tashen hankula da suka wakana a wannan kasa ta yankin tsakiyar nahiyar Afirka. Sai dai hukumomin Bangui sun kaddamar da wani shiri na raba 'yan tawayen Seleka da makamkai da suka mallaka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal