1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Touadera ya yi alkawarin hada kan yan kasa

Abdul-raheem Hassan
January 5, 2021

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera ya yi alkawarin tabbatar da hadin kai a kasar mai fama da rikicin addini da na kabilanci bayan lashe zabe wa'adi na biyu.

https://p.dw.com/p/3nVvH
Zentralafrikanische Republik Faustin Archange Touadera
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Da kuri'u kashi 53.9 ne shugaban mai shekaru 63 ya sake nasara a cewar hukumar zaben kasar ANE, sai dai a makon da ya gabata 'yan adawa sun bukaci soke zaben da suka kira mai cike da magudi.

A ranar Lahadin ta shige, 'yan tawaye sun karbe iko da birnin Bangassou mai tazanar kilomita 750 daga gabashin Bangui babban birnin kasar, a ranar Litinin kuma babban mai gabatar da kara na gwamnati ya kaddamar da bincike kan tsohon shugaban kasar Francois Bozize, kan zargin yunkurin kifar da gwamnati gabanin zabe.