1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta sayar da wasu kadarorinta

August 22, 2023

A wani abin da ke zaman alamun rikicin rashin kudin da ke gaban sabuwar gwamnatin Najeriya, gwamnatin ta ce tana shirin cefanar da wasu kadarori da nufin samun kudin tafiyar da harkokin mulkin kasar

https://p.dw.com/p/4VRnh
Matatar mai a Najeriya
Matatar mai a NajeriyaHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Sama da kaso 95 cikin dari na kudaden da ke zuwa aljihun gwamnatin tarayyar Najeriya ya na tafiya ne wajen biyan kudin ruwa da ma bashin da ya kai wa kasar iya wuya a halin yanzu. Sai dai kuma sabbin mahukuntan Najeriyar sun ce suna shirin sayar da wasu kadarorin gwamnatin kasar da nufin tara Dalar Amurka miliyan dubu 17 domin gudanar da harkokin mulki.

Babban Bankin Najeriya CBN
Babban Bankin Najeriya CBN

Karin bayani

Shirin sayar da kadarorin gwamnatin Najeriya ya janyo cece-kuce

Kama daga masana'antun karafa ya zuwa matatun mai na kasar dai, tarrayar Najeriyar na kallon kadarori da yawa a wani abin da ke nuna girman rashin kudin da ke gaban masu mulkin kasar. Akalla kaddarori 70 ne dai ke cikin rajistar gwamnatin kasar da sunan ciniki a Najeriyar da ke da nauyin bashi. Dr Isa Abdullahi kwarrare kan tattalin arzikin Najeriyar ya ce sabuwar dabarar na iya taimaka wa masu mulkin kasar.

Kokarin yadda kwallon mangoro, ko kuma wasoso da dukiyar al'umma dai, an dauki lokaci ana ta siyasa mai zafi kan batun kadarorin. Kuma kama daga 'yan kodago zuwa ga 'yan adawa, an yi nisa cikin kace nace kan cinikin kadarorin.

Kamafanin Iskar Gas na Najeriya
Kamafanin Iskar Gas na NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Tsohuwar gwamnatin Yar Adu'a alal misali ta yi watsar da cinikin matatun mai na gwamnatin Chief  Olusegun obasanjo bayan  adawa mai zafi a cikin kasar. 

Kokarin satar kudi, ko kuma cika alkawari ga 'yan kasa, ana kallon rage kashe kudi a bangaren masu mulki na iya kaiwa ga biyan bukata.