1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karbo bashi daga bankin duniya

Binta Aliyu Zurmi
September 30, 2022

A wani shirin na nemo mafita ga jihohin Najeriya 36 na rashin iya biyan albashi ga ma'aikatansu, bankin duniya ya amince da bai wa kasar bashin dala miliyan 750.

https://p.dw.com/p/4HayY
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Jihohi da dama a kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka na fama da rashin isasun kudaden shiga, matakin da ke kai su ga cin bashi domin biyan albashi da ma gudanar da wasu muhimman ayyukan raya kasa.

Bankin duniya ya ce Najeriya ta taimaka matuka wajen rage wahalhalun yin kasuwanci ga 'yan kasar, sai dai har yanzu an gaza yin nasarar shawo kan 'yan kasuwar kasashen ketare don habaka hannayen jari idan aka kwatanta da wasu kasashe. 

Ko baya ga biyan albashi da ke zama makasudin ciwo wannan bashi, kazalika za kuma a yi amfani da kudaden wajen samar da ayyuka ta hanyar kuwanci da kuma inganta hanyoyin sadarwar kasar gami da kyautata cinikayya tsakanin 'yan kasuwa da bangaren gwamnati.