1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tiani ba zai halarci taron kasashen Afirka a Chaina ba

September 2, 2024

A yayin da shugabannin kasashen Afirka suka hallara a Chaina a ranar Litnin domin taron diflomasiyya, wasu daga cikin jagororin nahiyar ba za su halarci taron ba.

https://p.dw.com/p/4kAFH
Hoton taron shugabannin Afirka da Chaina a 2018
Hoton taron shugabannin Afirka da Chaina a 2018Hoto: Li Tao/Photoshot/picture alliance

A ranar Litinin ne ake bude wani babban taro tsakanin shugabannin kasashen nahiyar Afirka da Chaina, da zummar yaukaka dangantaka tsakanin Chainar da kuma nahiyar dake dankare da albarkatun kasa.

Beijing ta ce wannan taron na mako guda shi ne irinsa na farko kan diflomasiyya tun bayan annobar Covid 19, wadda kuma shugabannin Afirka da dama ke halarta.

Taron Amirka da Afirka na daukan hankali

Chaina ta rika bai wa kasashen na Afirka bashin biliyoyin daloli da kuma ayyukan gina kasa. Kasar ta aike da dubban daruruwan ma'aikatanta zuwa Afirka domin yin manyan ayyuka, a yayin da ita kuma ta ke gutsura daga cikin albarkatun kasa da Allah ya huwace wa nahiyar irinsu zinare da azurfa da dai sauransu.

Taron tattalin arziki tsakanin Japan da Afirka

Daga cikin shugabannin kasashen na Afirka da ke halartar taron har da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango Felix Tshisekedi, sai dai shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tianibai samu damar halarta ba, amma ya tura Firaminstan kasar Ali Lamine Zeine a matsayin wakili.