1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da Nijar sun kulla sabuwar yarjejeniyar tsaro

August 29, 2024

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce sojojin Nijar da na Najeriya sun amince su gyara alakarsu domin yin hadin gwiwar yaki da matsalar tsaro da kasashen makwabtan juna ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4k3eh
Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Kasashen Nijar da Najeriya sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar karfafa tsaro a tsakaninsu, a karon farko tun bayan dagulewar diflomasiyya a tsakaninsu lokacin da soja Janar Abdourahamane Tiani ya tunkude zababbiyar gwamnati a shekarar da ta gabata.

Wannan dai na zuwa bayan ganawar da hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Musa Christopher da takwaransa na kasar Nijar Birgediya Janar Moussa Salaou Barmo ya yi a birnin Yamai na Jamhuriyar ta Nijar a Larabar da ta gabata.

Gabannin zaman dai, kungiyar bunkasa kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, a karkashin Najeriya ta yi barazana afka wa sojojin Nijar domin tilasta wa masu juyin mulkin dawo da hambararren shugaba Mohamed Bazoum, matakin da ya fusata gwamnatin mulkin sojin Nijar, ta kai ga ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS tare da kulla sabuwar alaka da kasashen Mali da Burkina Faso.