1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin tsaro lokacin zaben gwamnoni

Ubale Musa SB/ZMA
March 16, 2023

A yayin da masu kada kuri'a Najeriya ke shirin komawa ya zuwa zaben gwamnonin galibin jihohin kasar da 'yan majalisun jihohi ana fuskantar barazanar rashin tsaro.

https://p.dw.com/p/4Ofwn
Najeriya I Tsaro lokacin zabe
Tsaro lokacin zaben NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/dpa

Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancin ta dai daukacin Najeriya tana shirin sake daukar harami a cikin zagaye na biyu na zabukan kasar da ke shiri ya gudana. Akwai damuwa game da irin matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihohi da dama na kasar ganabin zaben na ranar Asabar da ke tafe (18.03.2023).

Karin Bayani: Martani kan dage zaben gwamnoni

Kimanin jihohi guda bakwai da suka hada da Kano da Lagos ko bayan Kaduna da Gombe da Jihar Zamfara da kuma jihohin Bauchi da Sokoto ne dai jami'an tsaron kasar suka ce na fuskantar barazana ta tayar da hankali a zabukan gwamnonin da ke tafe.

Najeriya | Zabe
Masu aikin zaben NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Ya zuwa yanzu dai kalamai da take-taken masu shirin taka rawa a yayin zaben dai na dada nuna alamun a mutu ko a yi rai cikin fagen na siyasar. Farfesa Rufa'i Alkali dai shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, jam'iyyar kuma da ke ta korafin fuskantar tayar da hankalin a yayin zaben gwamnan jihar kano.

Kokari na jan ido na masu siyasa, ko kuma neman cika burin mulki dai, in har NNPP na ganin da sauran sake, ita ma APC mai mulki a jmihar Kano ta ce ba ta goyon bayan tashin hankali cikin fagen siyasar. Zubar da jini a siyasa ko kuma tsoratar da masu adawa dai, zaben gwamnonin daga duk alamu na iya tasiri a daukacin fagen siyasar kasar.

Har ya zuwa yanzu dai Najeriya tana fuskantar kokarin dinke tsakani sakamakon zaben shugaban kasar da ya yi nasarar raba kai bisa turbar addini da kabilanci.