Yiwuwar kafa gwamnatin hadaka a Najeriya
March 13, 2023Duk da nasarar da zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben da aka yi a kasar, rarrabuwar kawuna na addini da ma yanki na ci gaba da zama babban kalubale ga siyasar kasar da ma gwamnatin da za'a kafa nan da watanni biyu masu zuwa. Abin da ya sanya yunkuri da ma hasashe na kafa gwamnatin hadin kan kasa a Najeriyar da zababbane shugaban kasar ke son yi. Wannan mataki ya haifar da tunani da ma fata daga alummar kasar a yanzu.
Tun bayan da ya samu nasarar lashe zaben na Najeriya da ya kasance cike da kace-nace a kansa, zababben shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamiti don zwarcin manyan ‘yan takarar da suka yi hamaiyya amma ya tikasu da kasa, koda yake sun da ja a kan nasarar. Shin wane tasiri wannan zai iya yi ga siyasar Najeriyar da ma gwamnatin da ake shirin kafawa a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, lokacin da Tinubun zai dare karagar mulkin Najeriya da ya dade yana kishirwar ganin haka?
Zababben shugaban Najeriyar da ke da salo na nima lokacina ne a barni in dana na fusknatar kalubalantara da manyan abokan hamiyyarsu biyu ke yi a kotu, bisa tabbabar nasara da ya samu, inda a yanzu ake share fage don tattake wuri a kotun daukaka kara.
A lokutan baya dai Najeriyar ta ga irin wannan salon a kafa gwamnatin hadin kasa inda aka jawo jamiyyun adawa tare da ba wasu mukami.
A wata zantawa da shi tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar da ya yi takara da zababben shugaban Najeriyar yace in an aiko mashi da goron gayyata zai duba tare da shawara ga jamiyyarsa ta PDP. Za'a sa ido a ga yiwuwar faruwar haka a siyasar Najeriyar mai cike da sarkakiyar gaske.