1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce tsakanin Nijar da kasar Mali

Gazali Abdou Tasawa LMJ
July 13, 2021

Tankiyar da ke zafafa tsakanin gwamnatin Mali da ta Jamhuriyar Nijar dangane da kalaman da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ya furta kan sojojin Mali, na yin barazana ga makomar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3wQpy
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed BazoumHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Ta dai kai gwamnatin Mali ta bukaci jakadan Nijar a Bamako ya bayyana a gabanta, domin bayyana rashin amincewarta da kalaman shugaban kasar ta Nijar Mohamed Bazoum yayin da al'ummar kasashen biyu ke ci gaba da musayar munanan kalamai a shafukan sada zumunta. Sai dai kuma wasu 'yan Jamhuriyar ta Nijar, sun soma kiraye-kirayen kasashen biyu su kai zuciyoyi nesa.

Karin Bayani: Kafa rundunar sintiri ta Turai a Sahel

Cece-kuce tsakanin kasashen biyu dai, ya samo asali ne daga kalaman da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ya furta a makon da ya gabata ga manema labarai a birnin Paris na Faransa, inda ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yadda sojojin Mali ke kokarin yin juyin mulki a kasarsu ba tare da yin wani katabus a fagen yaki da 'yan ta'addan da suka mamaye kasarsu da kuma ke shafar Nijar din kai tsaye ba. Sai dai da yake tsokaci kan wannan batu, Malam Garre Amadou editan jaridar La Nation cewa ya yi shi bai ga abin tayar da jijiyoyin wuya ba, domin gaskiya Shugaba Bazoum ya fada.

Mali Ankunft Assimi Goita
Sau biyu cikin kasa da shekara guda, sojoji suka yi jujyin mulki a MaliHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/MAXPPP/dpa/picture alliance

Yanzu haka dai sojojin Nijar sama da 800 ne a kasar ta Mali tun bayan ceto ta daga hannun kungiyoyin 'yan ta'adda, wadanda suka yi yunkurin kwace birnin Bamako a shekara ta 2012. To sai dai a daidai loakcin da wasu 'yan Nijar ke nuna goyon bayansu ga shugaban kasarsu, kungiyar tsofaffin manyan jami'an gwamnati wato CIRAC, ta bakin shugabanta Malam Idi Ango Omar kira ta yi ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa da tunkarar juna domin yin sulhu.

Karin Bayani: Sabuwar tawagar ECOWAS a Mali domin sulhu

Da yake mayar da martini kan bacin ran shugabanni da ma wasu 'yan kasar Malin kan kalamansa, Shugaba Mohamed Bazoum cewa ya yi: "Ba zan taba sauya ra'ayina a kan Mali ba, kuma ko gobe zan kare ta ba tare da la'akari da wa ke shugabancinta ko ta wace hanya ya karbi mulki ba. Mali makwabciyarmu ce kamar Burkina Faso da Chadi da sauran kasashe da makomarmu ta zamo daya. Duk lokacin da daya daga cikin kasashen ke da matsala, tana shafarmu ne kai tsaye. Kuma duk da ka'idojin diplomasiyya, mu kan fadawa junanmu gaskiya. Domin wannan shi ne zaman tare kuma zaman gaskiya, mai son ka shi ke fada maka gaskiya".

Kokarin jin ta bakin 'yan Mali mazauna Jamhuriya Nijar kan wannan cece-kuce ya ci tura, inda da dama suka ce ba su da ta cewa.