1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta gaza shawo kan rikicin Mali

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 24, 2020

Halin rikicin da kasar Mali ke ciki, na ci gaba da  daukar hankulan kasashen duniya da ke kai kawo wajen neman samun mafita, ta baya-bayan nan ita ce kungiyar ECOWAS ko CEDEAO.

https://p.dw.com/p/3fsMy
Krise in Mali | ECOWAS | Muhammadu Buhari und Boubou Cissé
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Firaminista Boubou Cissé na MaliHoto: Présidence du Mali

Ita dai kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Afirka ta Yamman wato ECOWAS ko CEDEAO ta tura wata tawaga zuwa Malin, inda ta gana da shugaban kasar da ma bangaren da ke adawa, domin samun sulhu. Tabarbarewar al'amura a kasar ta Mali saboda taron dangin da kungiyoyin 'yan adawa da ma masu rike da makamai suka yi wa shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ne dai, ya sanya kungiyar ta Ecowas tura tawagar ta musamman a wannan kasa da ke cikin hali na rudani da rashin tabbas tun daga 2012. Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya ce lamarin fa ya wuce batun adawa kawai.
A Alhamis din wannan makon dai, wata tawagar kungiyar kasashen ECOWAS ko CEDEAO din a karkashin jagorancin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa Bamako babban birnin kasar ta mali, da nufin kawo shawarar kafa gwamnatin hadin kan kasa, abin da a fili shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ba ya maraba da shi, domin yana da sauran shekaru uku a wa'adin mulkinsa. Amma bisa kimar da mambobin tawagar ta ECOWAS ko CEDEAO ke da ita, ko za ta samar da wani chanji? 

Mali Bamako Anti Regierungsproteste
Kasar Mali t a tsunduma cikin rikicin siyasaHoto: picture-alliance/AP Photo/B. Ahmed

Mali dai kasa ce mai muhimmanci ga kasashen Afrika ta Yamma da ya zama dole a nemo mafita kamar yadda Barrsiter Mainasara Umar mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya nunar. Ana dai jiran ganin ko shiga tsakanin na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO zai iya kai wa ga sulhunta rikicin na Mali wanda nahiyar Turai da Amirka suka yi iya nasu kokari na samar da mafita.