1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bukatar sake dubarar yaki da 'yan ta'adda

Gazali Abdou Tasawa MNA
May 18, 2021

Kungiyar wasu tsoffin jami’an gwamnatin Nijar da aka fi sani da CIRAC, ta bukaci gwamnati da ta bayar da bahasi a kan wasu batutuwa da ke daure wa 'yan kasar kai a yakin da ake yi da ta’adda.

https://p.dw.com/p/3tYvf
Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A sanarwar da ta fitar kungiyar mai suna Cercle Independant de reflexion et d'action wato CIRAC a takaice, wacce ta kunshi tsoffin manyan jami'an gwamnati masu da'awar nazarin shawo kan matsalolin Nijar ta soma ne da dora ayar tambaya a kan yadda Nijar ke kin amfani da jiragen yakin da ta mallaka a yakin da take da kungiyoyin 'yan ta'adda musamman kan iyaka da Mali kamar dai yadda shugaban kungiyar ta CIRAC Omar Idi Ango, tsohon ministan tsaro na kasar Nijar ya yi karin bayani.

"A lokacin mulkin Issoufou Mouhamadou akwai jiragen yaki da aka saye wajen biyar zuwa shida, musamman saboda sojojin kasar Nijar. Don me 'yan tarzoma za si shiga gari su kwashe awanni da dama suna cin karensu babu babbaka, amma ba a kai musu hari ba."

Karin bayani: Nijar: Kokarin shawo kan matsalar tsaro

Wani batun da kungiyar ta CIRAC ta ce yana daure mata kai a yakin da Nijar take da ta'addanci shi ne yadda kasancewar sojojin kasashen duniya a yankin ya kasa yin tasiri wajen dakile matsalar ta'addancin shekaru da dama.

Sojojin Nijar da ke sintiri a kan hanyar Agadez da Arlit inda 'yan bindiga ke garkuwa da Turawa
Sojojin Nijar da ke sintiri a kan hanyar Agadez da Arlit inda 'yan bindiga ke garkuwa da TurawaHoto: Getty Images/AFP

Kungiyar ta CIRAC ta ce amma babban abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya shi ne irin yadda mahukunta da jami'an tsaro ke kin kawo dauki ga al'ummomin kauyukan kan iyakokin kasar duk da irin yadda suke sanar da su a duk lokacin da suka samu labarin shirin zuwan maharan.

Shugaban Kungiyar ta CIRAC Omar Idi Ango ya kuma bayar da shawarwari na irin matakan da mahukunta ya kamata su dauka domin dakile matsalar ta'addanci.

Karin bayani: Matsalar tsaro na karuwa a Tillaberi da ke Nijar

"Ya kamata a binne nakiyoyi a iyakar kasarmu da kasar Mali. Sojojin suna iya yin taswira na wuraren da nakioyinsuke tsakaninmu da Mali. Kuma a kafa wuraren binciken ababen hawa da ma mutane kamar biyu ko uku inda dole mutum ya bi ta nan, idan bai bi ta nan ba, to sai dai ya bi ta inda nakiya take, ta kuma tashi da shi."

Kazalika kungiyar ta CIRAC ta bukaci sabuwar gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da ta kira babban taron muhawara na kasa kan hakokin tsaro wanda ta ce tana kyautata zaton zai fitar da shawarwarin da za su taimaka ga shawo kan matsalar tsaron a Nijar da ma yankin Sahel baki daya.