1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya za ta dauki mataki a kan ba da biza

Uwais Abubakar Idris AH
October 23, 2023

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa daga yanzu za mayar da martani a kan duk kasar da take kin bai wa ‘yan kasar takardar izinin shiga kasarta.

https://p.dw.com/p/4XuEb
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Aka ce dai ta kama hanyar cimma ruwa domin bayan kwashe shekaru ne ana muzgunawa ‘yan Najeriyar da ke neman takardun biza na shiga kasashen dunioya ne gwamnatin Najeriyar ta dauki wannan mataki. Ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriyar Olubunmi Tunji-Ojo dai ya bayyana cewa lokaci ya wuce da Najeriyar za ta rinka bai wa 'yan wasu kasashe izinin ziyarar kasar amma kuma a yi wa kasar kememe. Ministan ya ce daga yanzu Najeriyar za ta maida martani. 

 'Yan Najeriya na wahala wajen samun bisa na wasu kasashen

Nigeria Abuja | Nigerianische Studenten geflüchtet aus der Ukraine
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Amma me tsarin dokokin Najeriya ya tanadar a kan irin wannan lamari da ministan kula da harkokin cikin gidan Najeriyar mai kazar- kazar ya dauka? Barrister Mainasara Umar masani ne a wannan fannin ya ce wani abu ne da ba a saba yi ba a kasar. Najeriyar dai ta bullo da shirye-shirye na gyara hallayen 'yan kasar don su zama jakadu na gari musamman wanda ma'aikatar wayar da kan jama'a ke yi. Ofisoshin jakadanacin wasu kiasashen da ke Najeriya musamman na nahiyar Turaisun zama tamkar wata kasauwa, inda ‘yan kasar kan yi tururuwa don neman bisa da ba kasafai suke samunta ba duk da kashe makudan kudadde da suke yi. To sai dai ga Ambassada Suleiman Dahiru kwararre a fanin diplomasiyya kuma tsohon amabasadan Najeriya a kasashen da dama ciki har da Sudan sai an jira an ga sakamakon matakin.

Ana kallon mataki a matsayin wani martani wanda zai yi tasiri

Nigeria Abuja | Nigerianische Studenten geflüchtet aus der Ukraine
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Duk wannan ta maza da ministan ya yi bayan dadewa ‘yan Najeriyar na korafi a kai, Ko menene yiwuwar iya daukan wannan mataki a halin da ake ciki a yanzu? Dr Kabiru Danladi Lawanti mai sharhi ne a kan siyasar kasa da kasa da ke jami'ar Ahmadu Bello a Zaria wanda ya ce matakin ya dace. A yayin da manyan jami'ai da masu hannu da shunni da kan shiga matsalar jinkirin samun takardar bisa, kan samu taimako ta ma'aikatar kasashen waje, ga mafi yawan ‘yan Najeriya ba su da wata madafa a kan al'amarin, abin da ya sanya  fatar samun tasirin lamarin.